24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Ba za mu bar ‘yan Najeriya zuwa Ukraine don yakar Rasha ba, Gwamnatin tarayya

LabaraiBa za mu bar ‘yan Najeriya zuwa Ukraine don yakar Rasha ba, Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta ce ba za ta juri ganin ‘yan Najeriya suna tafiya kasar Ukraine a matsayin mayakan da zasu taya ta fada da Rasha ba, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda takardar da kakakin ministan harkokin kasashen waje, Francisca Omayulo ya saki a ranar Litinin, 7 ga watan Maris, gwamnati tana kan tattaunawa da Ukraine don dakatar da ‘yan Najeriya daga shiga fadan Ukraine.

Ba za mu bar ‘yan Najeriya zuwa Ukraine don yakar Rasha ba, Gwamnatin tarayya
Ba za mu bar ‘yan Najeriya zuwa Ukraine don yakar Rasha ba, Gwamnatin tarayya

Takardar ta zo ne bayan ‘yan Najeriya sun yi caa a ofishin jakadancin Ukraine da ke Abuja bayan shugaban kasar Ukraine ya yi kira akan mutanen duniya su kai musu dauki.

Kamar yadda takardar tazo:

“An janyo hankalin gwamnatin tarayyar Najeriya akan yadda ‘yan Najeriya suke ta rijista don zuwa yaki a matsayin sojojin Ukraine a Ofishin jakadancin kasar da ke Abuja.

“Ma’aikatar harkokin kasashen waje ta tuntubi ofishin inda ta samu tabbaci. Ofishin jakadancin Ukraine ta musanta wannan zargin inda tace tabbas ‘yan Najeriya da dama sun je har ofishin inda suka bayyana cewa a shirye suke da su taya Ukraine yakar Rasha.

“Ofishin ya ci gaba da tabbatar da cewa gwamnatin Ukraine bata bukaci wani dan kasar waje da ya kai mata dauki ba, kuma bata bukaci biyan $1,000 ba daga hannun wani mayaki don kudin jirgi.

“Najeriya ba za ta lamunci hakan ba kuma ba za ta jure ganin wani dan Najeriya yana kokarin zuwa a matsayin mayakin da zai taya Ukraine ko wata kasa a duniya yaki ba.

“Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da hada kai da ofishin jakadancin Ukraine da ke Najeriya da kuma duk wasu hukumomi don dakatar da hakan.”

Da ɗumin sa: Jirgin farko ɗauke da ‘yan Najeriyan dake Ukraine ya iso Abuja

Sahun farko na jirgin da ke ɗauke da ‘yan Najeriyan da su ka maƙale a ƙasar Ukraine ya iso gida Najeriya.

Sun iso gida Najeriya ne daga ƙasar Romania a safiyar ranar Juma’a. Jaridar PUNCH ta rahoto

Hukumomi sun tabbatar da isowar su

Shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya da ke zama a ƙasashen waje, Abike Dabiri Erewa, ta tabbatar da hakan a wata wallafa da tayi a shafin Twitter.

A ranar Laraba da ta gabata ne gwamnatin taryya ta amince da dala miliyan 8.5 domin gaggauta kwaso yan Najeriya 5,000 da ke makale a ƙasar Ukraine a sakamakon yakin da ƙasar  Rasha ta ƙaddamar akan ƙasar Ukraine.

An kwaso jimillar mutane 411, waɗanda su ka haɗa sa ma’aikatan ofishin jakadancin Najeriya a ƙasar Ukraine da kuma sauran ‘yan Najeriya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe