24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Hukuma ta yi ram da matar da ta halaka yaran ta 2 ta hanyar zuba musu guba a abinci

LabaraiHukuma ta yi ram da matar da ta halaka yaran ta 2 ta hanyar zuba musu guba a abinci

‘Yan sanda sun kama wata mata a Mwiyala dake kusa da birnin Kakamega a kasar Kenya, mai shekaru 32, wacce ta halaka yaran ta, ta hanyar zuba musu guba a abinci, LIB ta ruwaito.

Pherine Maero, wacce ma’aikaciyar jinya ce, ta zuba wa yaran ta guda biyu guba, ‘dan shekara bakwai da dan shekara tara, a daren Asabar, 5 ga watan Maris, inda daga bisani ta kira tsohon mijin nata, da ya zo ya amsa gawar yaran nashi.

woman who killed her children

Charles Akhonya, mai gadin gidan su ya ce, matar ta tunkaro shi a kofar gidan misalin karfe 3:00 na dare, inda ta bukaci ya bude wa mijin kofar, sai dai ko da ya bisu cikin gidan, ya ga gawar yaran a kan gadon su.

An ceto rayuwar matar, wacce tayi kokarin daba wa kan ta wuka a wuya, yayin da take samun kulawa a asibitin Kakamega, kamar yadda ‘yan sanda ke bincikar lamarin.

Makwabtan, sun bayyana wa manema labarai yadda matar ke al’amura cikin rashin hankali tun lokacin da ta rabu da mijin ta, akwai lokacin da ta rotse motar mijin nata bayan ya ajiye ta a gidan.

Kakamega Central OCPD Valerian Obore ne suka tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka bayar da labarin yadda wacce ake zargin take kwance a asibiti, kuma za a gurfanar da ita bisa zargin ta da laifin kisan kai bayan ta samu sauki.

An dauki gawar yaran daga Babban asibitin koyarwa na Kakamega zuwa ma’adanar gawa.

Saurayi ya halaka budurwarsa, ya kira ‘yan uwanta ya sanar musu sannan ya cika wandonsa da isa

Ana zargin wani saurayi da kashe budurwarsa a Abuja, ya kuma sanar da ‘yan uwanta cewa “su zo su dauki gawar ta”.

A watan Mayun 2021, kuma ya shiga cikin watan Agusta na wannan shekarar, an bayyana cewa wanda ake zargin ya koma gidan marigayiyar ne saboda ba shi da aikin yi kuma ba shi da wurin kwana.

An ruwaito cewa Evelyn ta sauke nauyin kudi na Ugochukwu, wanda aka ce ya yi mata fyade ko kadan.

Ta yi shirin ficewa daga falon saboda cin zarafinta da yake yi. Sai dai kuma a ranar Asabar, 19 ga watan Fabreru, sun samu saɓani inda ya shaƙe ta har lahira ya gudu.

“Bayan ya gudu zuwa wani wurin ɓuya, Ugochukwu ya kira mahaifin Evelyn a kauyen yana tsoratar da shi game da mutuwar Evelyn, cewa ya zo ya ɗauki gawar ‘yarsa.

“Ya kuma kira wani surikin sa ya ce masa haka. Uban ne ya kira daga ƙauye ya sanar da ‘yan uwa a Abuja. Haka labarin ya kasance.” Wata majiya ta ce.


Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan sanda sun gano gawar ta a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu.

Abokan marigayiyar sun yi ta yadawa a shafukan sada zumunta na yanar gizo suna jimamin rasuwar ta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe