Tarihin Mary Ann, matar da ta lashe gasar muni ta duniya

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
You are currently viewing Tarihin Mary Ann, matar da ta lashe gasar muni ta duniya
Tarihin Mary Ann, matar da ta lashe gasar muni ta duniya

Mary Ann ce matar da ta lashe gasar muni ta duniya inda ta samu makudan kudade bayan jerawa da munana da dama wadanda suka fito daga yankuna daban-daban.

Asali ba mummuna bace, hasali ma ma’aikaciyar asibiti ce, sai dai sakamakon wata cuta da ta same ta, halittar ta gaba daya ta sauya, kamar yadda shafin The Enigma na Facebook ya ruwaito.

Sakamakon sauyin halittar, mutane da dama sun dinga zunden ta inda ta zama abar dariya.

mary ann da yaran ta
Tarihin Mary Ann, matar da ta lashe gasar muni ta duniya

A baya, kwararriyar ma’aikaciyar jinya ce a asibTarihin Mary Ann, matar da ta lashe gasar muni ta duniyaiti, tana zaune cikin rufin asiri da mijin ta tare da yaran ta guda 4.

Wata rana ta wayi gari tana jin sauyi na daban a jikin ta tare da radadi a fuskar ta. Ashe daga lokacin rayuwar ta zata sauya gaba daya.

Bata san zata zama mace mafi muni a duniya ba

Nan da nan jikinta ya fara sauyawa, kuma cikin kankanin lokaci aka kore ta a aiki sannan mijin ta ya rasu inda ya bar ta da yara 4.

Sai dai Ubangiji ya yi gaggawar kawo mata mafita. Duk da dai ta yi kokarin komawa aiki amma ba a amince da ita ba don gudun yaduwar cutar da ke damun ta.

Sai da ta karanta jarida wacce taga batun gasar muni, nan da nan ta yanke shawarar shiga gasar wacce ta lashe.

Ta shiga cikin munanan da ke Ingila wanda ta lashe gasar har aka ba ta mukudan kudade. Bayan lashe gasar, ta samu aiki take yanke.

Ta san ba za ta taba ci gaba da aikin jinya ba har abada. Nan da nan aka dinga yada hotunan ta, wasu suna dariya duk da rashin sanin nata munin na cuta ne.

Aka dinga kiran ta “mace mafi muni a duniya”.

Sai dai komai yana da dalilin sa, an gano tana da cutar “Acromegaly”, wacce take janyo gabobin dan adam su dinga girma ba bisa ka’ida ba.

Manyan Kasashen duniya 10 da suka fi sauran kasashe arzikin man fetur a shekarar 2022

Idan aka ga wani batu da ya shafi arzikin man fetur na kasashe daban-daban, hankali yana karkata kan kasar Saudiyya domin an san cewa za ta kasance kan gaba, amma abin mamaki ba haka zancen ya ke ba.


Ga jerin jaddawalin kasashe 10 da ke da arzikin mai, wanda kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta fitar. Jimillar arzikin mai a duniya an kiyasta ya kai ganga tiriliyan 1.48.

  1. Venezuela kasar tana samar da mai kimanin biliyan 304,sannan a kowace rana tana fitar da mai ganga 2,489


2. Saudiyya-kasar saudiyya tana samar da mai kimanin biliyan 259,sannan a ko wacce rana tana fitar da ganga 11,545.7 na mai.
3. Iran-kasar iran tana samar da mai kimanin biliyan 209 wanda a kowacce rana tana fitar da ganga 3,538 na mai

4. Iraqi – kasar Iraqi tana samar da mai biliyan 145 sannan a kowacce rana tana fitar da ganga 2,986.6 na mai

5. Kuwait – kasar Juwait tana fitar da mai kimanin biliyan 102,sannan a kowacce rana tana fitar da ganga 2,796.8 na mai.

6. Daular Larabawa – Daular larabawa tana iya samar da mai kimanin biliyan 98 sanan tana fitar da ganga 3,213.2 na mai a kowacce rana.


7. Rasha – kasar Rasha tana samar da mai kimanin biliyan 80,wanda a kowacce rana tana iya fitar da mai kimanin ganga 10,397a kowacce rana.

8. Libiya – kasar Libiya ta na samar da mai biliyan 48,sannan a kowace rana tana fitar da mai ganga 1,483.

9. Najeriya – Najeriya tana da mai kimanin biliyan 37 sannan a kowacce rana tana fitar da mai ganga 2,524.1

10. Amurka -kasar Amurka bata kasance kasa mai arzikin mai ba amma ta kasance kasar da take iya sarrafa mai wanda ya kai kimanin ganga Biliyan 47

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi