29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

An kama Ummi Rahab ta bogi a Kano ta damfari wani dan kasar Amurka

LabaraiKannywoodAn kama Ummi Rahab ta bogi a Kano ta damfari wani dan kasar Amurka

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke wata sananniyar jarumar wasan Hausan nan Ummi Rahab, amma fa ta bogi.

Tun da fari dai wani mazaunin kasar Amurka dan asalin jihar Kano ne ya shigar da karar ta ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta hannun abokinsa kan cewar, sun hadu da matashiyar da take amfani da sunan Ummi Rahab a shafin sada zumunta na Facebook.

A haka a haka har soyayya ta kullu a tsakaninsu, inda matashin ya kuduri aniyar angwancewa da jaruma Ummi Rahab.

Bayan daukar wasu lokuta yana kashe mata makudan kudade ya gano cewa ashe dai ba ita bace Ummi Rahab ta asali ba, kawai dai ta zo ne domin ta kwace masa ‘yan kudaden shi.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyanawa jaridar Nagartaciyya cewa daga lokacin da suka samu wannan korafi suka shiga bincike har Allah ya basu nasarar kamo matashiyar tun ba a je ko ina ba.

Matashiyar da aka kama mai suna Nusaiba Yahya ‘yar shekaru 18 dake zaune a unguwar Hotoro ta tabbatar da cewa hakika ta bude shafin Facebook da sunan Ummi Rahab, wanda hakan ya bata damar yaudarar wancan matashi mazaunin kasar Amurka tare da karbe masa kudade.

Haka zalika SP Kiyawa ya tabbatar da cewa za su sanar da ‘yan jarida halin da ake ciki da zarar sun kammala bincike a matakin farko, kafin a gurfanar da matashiyar gaban kuliya domin girbar abinda ta shuka.

An sa ranar auren Lilin Baba da jaruma mai tasowa, Ummi Rahab

Yayin da mutane suke ta jita-jita da surutai akan cewa ‘yan fim ba sa auren junan su, Lilin Baba da Ummi Rahab zasu karya wannan rantsuwar ta’yan fim ba sa auren juna, don yanzu haka an sanya ranar auren su.

A rana Juma’a, 4 ga watan Maris Tashar Tsakar Gida ta YouTube ta wallafa batun sa ranar auren nasu.

Yanzu haka duk wasu shirye-shirye sun kankama akan cewa Lilin Baba zai angwance da amaryarsa, Ummi Rahab bayan sallah mai zuwa.

Tashar Tsakar Gida ta samu labari akan cewa manyan jarumai kamar Ali Nuhu ne suka shige wa mawakin gaba akan neman auren auren Ummi kuma an ba su auren ta.

Ba don wani akasi da aka samu ba da tuni an daura auren kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta tattauna da daya daga cikin waliyyan amarya, Yasir Ahmad wanda ya tabbatar da cewa za a daura auren bayan sallah.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe