Zamu ƙulla kawance mai ƙarfi da ƙasar Isra’ila -Yariman Saudiyya

  • Post author:
  • Reading time:4 mins read
You are currently viewing Zamu ƙulla kawance mai ƙarfi da ƙasar Isra’ila -Yariman Saudiyya

Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman yayi tsokaci kan dangantakar da ke a tsakanin Saudiyya da ƙasashen Isra’ila, Iran da Qatar. Yariman yayi wannan tsokacin ne yayin wata zantawa da jaridar The Atlantic.

Dangatakar Saudiyya da Isra’ila

A cewar yariman, hanyar kawai da ƙasar Isra’ila za ta iya ƙulla ƙawance da ƙasar Saudiyya shine idan har Isra’ila ta warware rikicin da ke tsakanin ta Palasɗinawa. Saudiyya tana kallon Isra’ila a matsayin ƙasar da za ta iya ƙulla kawance da ita idan har ta daidaita lamura tsakanin ta da Palasɗinawa. Jaridar Life In Saudi Arabia ta rahoto

Dangantaka tsakanin Saudiyya da Iran

Yariman Saudiyya ya tabbatar da cewa Saudiyya na duba yiwuwar tattaunawa da ƙasar Iran ta yadda ƙasashen biyu za su cimma daidaito wanda kowace ƙasa za ta aminta da shi a tsakanin su.

Ya kuma yi fatan kaiwa ga matakin da zai sanya ƙasashen biyu samun daidaito wanda zai sanya goben su tayi kyau.

Da yake magana kan shirin makamashin nukiyar ƙasar Iran, Yariman Saudiyya ya bayyana cewa ƙasashen biyu ba za su iya watsar da juna ba. Ya bayyana cewa zama tare tsakanin makwabtan biyu shine maslaha kawai.

Yariman Saudiyya yana ganin cewa mallakar bam ɗin nukiliya ne ƙasar Saudiyya ba ta son Iran ta yi.

Dangantaka tsakanin Saudiyya da Qatar

Yariman na Saudiyya yayi farin cikin samar da cewa dangantakar dake tsakanin Saudiyya da ƙasar Qatar mai kyau ce, inda ya bayyana sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, a matsayin mutumin kirki.

Matukin jirgin kasar Saudiyya ya mutu yana tsaka da tuki daga Bisha zuwa Riyadh

A yau za mu kawo muku cikakken labarin wani matukin jirgin ƙasar Saudiyya wanda ya rasu a cikin jirgin SV 1734 kafin ya sauka a filin jirgin sama na Riyadh.

A ranar 1 ga Maris 2016, Jirgin SV 1734 ya tashi a kan lokaci daga tashar jirgin saman Bisha kuma ya daure ya sauka a filin jirgin saman Riyadh dake Saudiyya. Komai ya kasance kamar yadda aka tsara, kamar yadda al’ada ta yau da kullum kuma wanda ba zai iya tsammanin cewa wani abu mara kyau zai faru ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Rubuta Sharhi