‘Yan bindiga sun yi awon gaba da amarya akan hanyar kai ta gidan miji a jihar Neja

  • Post author:
  • Reading time:4 mins read
You are currently viewing ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da amarya akan hanyar kai ta gidan miji a jihar Neja
Niger: 'Yan ta'adda sun yi garkuwa da amarya a wajen bikin aurenta, sun kashe wasu 10

Wata sabuwar amarya ta faɗa a hannun ‘yan bindiga akan hanyar kai ta zuwa gidan mijin ta a jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta samo cewa ‘yan bindigan sun kawo harin ne lokacin da ‘yan’uwan amaryar su ka ɗauko ta daga ƙauyen Allawa a ƙaramar hukumar Shiroro zuwa garin Pandogari, a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar.

‘Yan bindigan waɗanda su ka zo da yawa sun farmake su a hanya, sannan su ka ɗauke amaryar da sauran mutanen da ke wajen a cikin wata babbar mota.

Shugaban majalisar matasan Lakpma, Jibrin Abdullahi Allawa, ya bayyana cewa lamarin ya auku ne ranar Juma’a.

Sun sake kai hari a wani ƙauyen

A cewar wata majiya, ‘yan bindigan waɗanda kuma su ka sace shanaye masu yawa sun kai wani harin a ƙauyen Gyaramiya, har ila yau cikin Shiroro, inda su kayi awon gaba da wasu daga cikin mazaunan ƙauyen.

Lamarin na zuwa kwanaki ƙadan bayan gwamnatin jihar ta bayar da sanarwar cewa ta samo nasara sosai akan ‘yan bindiga.

Ba a samun jin ta bakin ‘yan sanda ba

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ba a samu jin ta bakin sa ba a wayar tarho.

Wannan dai ba shi bane karo na farko da harin ‘yan bindiga ya ritsa da amare ba a jihar.

Ko a satin da ya wuce, sai da aka ɗauke wasu amare guda biyu a ƙaramar hukumar Lavun ta jihar Neja.

Miyagun ‘yan bindiga sun yi garkuwa da amarya da wasu mutum 5 a Kaduna

Wasu miyagun ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Rigachikun da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da wata amarya da aka kusa auren ta da wasu mutane biyar.

An rawaito cewa ‘yan bindigar sun afkawa al’ummar da ke kusa da madatsar ruwan kasan da misalin ƙarfe ɗaya na safiyar ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu, inda suka far wa gidaje uku tare da tasa ƙeyar waɗanda abin ya shafa zuwa inda ba a sani ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi