Harin bam ya halaka mutum 30 a wani masallacin Juma’a a Pakistan

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Harin bam ya halaka mutum 30 a wani masallacin Juma’a a Pakistan

Aƙalla mutum 30 ne su ka riga mu gidan gaskiya bayan tashin wani bam a yankin Qissa Khwani Bazaar, a Peshawar, ƙasar Pakistan. Za a iya samun ƙaruwar waɗanda su ka samu raunika, yayin da asibitoci su ke cikin shirin ko ta kwana.

Wasu mahara guda biyu sun yi ƙoƙarin ƙutsawa cikin masallacin kafin nan su ka buɗe wuta kafin aukuwar harin ƙunar baƙin waken. Jaridar The Islamic Information ta rahoto

An bada umurnin kai agajin gaggawa

Firaministan ƙasar Pakistan, Imran Khan, ya bada umurnin bayar da agajin gaggawa ga waɗanda su ka samu raunika.

An kai waɗanda harin ya ritsa da su zuwa asibitin Lady Reading Hospital.

Lady Reading Hospital 768x576 1
Harin bam ya halaka mutum 30 a wani masallacin Juma’a a Pakistan. Hoto daga The Islamic Information

Sojojin Pakistan sun sanya shinge a yankin

Sojoji sun isa wurin inda su ka sanya shinguna domin cigaba da gudanar da bincike.

Harbe-harben yayi sanadiyyar rasa ran wani jami’in ‘yan sanda kafin aukuwar harin ƙunar baƙin waken a cikin masallacin.

Masallata na cikin tsaka da gabatar da sallar Juma’a lokacin da bam ɗin a fashe a cikin masallacin.

CCPO na Peshawar ya tabbatar cewa an saka bam ɗin ne a Imambargah a cikin Kocha Risaldar. Ya ƙara tabbatar da cewa harin ƙunar baƙin wake ne yayin da aƙa bindige ɗan sanda guda ɗaya.

Aƙalla mutane 21 sun rasa rayukansu bayan dusar ƙanƙara ta faɗo musu a Pakistan

Pakistan – Dusar ƙanƙara ta kashe aƙalla mutane 21 bayan motocin su sun maƙale yayin da dubunnan baƙi masu yawon buɗe ido su ka garzaya garin Murree na ƙasar Pakistan.

Da yawa daga cikin waɗanda abin ya ritsa da su sun rasu ne a dalilin Hypothermia, kamar yadda jami’ai suka bayyana. A cikin su akwai wani ɗan sandan Islamabad da mutane bakwai cikin iyalan sa, kamar yadda ɗan sanda Atiq Ahmed ya shaida.

Fiye da ƙafa 4 (122cm) na dusar ƙanƙara ta faɗa tsaunin Murree da ke Pakistan a ranar Juma’a da dadare da kuma safiyar Asabar, inda motoci da dama suka maƙale a kan hanya, a cewar ministan cikin gida, Sheikh Rashid Ahmed.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

This Post Has One Comment

Rubuta Sharhi