29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

An sa ranar auren Lilin Baba da jaruma mai tasowa, Ummi Rahab

LabaraiKannywoodAn sa ranar auren Lilin Baba da jaruma mai tasowa, Ummi Rahab

Yayin da mutane suke ta jita-jita da surutai akan cewa ‘yan fim ba sa auren junan su, Lilin Baba da Ummi Rahab zasu karya wannan rantsuwar ta’yan fim ba sa auren juna, don yanzu haka an sanya ranar auren su.

A rana Juma’a, 4 ga watan Maris Tashar Tsakar Gida ta YouTube ta wallafa batun sa ranar auren nasu.

An sa ranar auren Lilin Baba da jaruma mai tasowa, Ummi Rahab
An sa ranar auren Lilin Baba da jaruma mai tasowa, Ummi Rahab

Yanzu haka duk wasu shirye-shirye sun kankama akan cewa Lilin Baba zai angwance da amaryarsa, Ummi Rahab bayan sallah mai zuwa.

Tashar Tsakar Gida ta samu labari akan cewa manyan jarumai kamar Ali Nuhu ne suka shige wa mawakin gaba akan neman auren auren Ummi kuma an ba su auren ta.

Ba don wani akasi da aka samu ba da tuni an daura auren kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta tattauna da daya daga cikin waliyyan amarya, Yasir Ahmad wanda ya tabbatar da cewa za a daura auren bayan sallah.

Baya ga hakan, akwai wani bidiyo da jaruma Umma Shehu ta wallafa wanda ya kara tabbatar da hakan wanda aka ga Lilin Baba da Amaryar tasa cike da farin ciki, a karkashi ta sanya “our next couple”.

Da dumin sa: Mawaki Lilin Baba yana shirye-shiryen auren jaruma Ummi Rahab

Fitaccen mawaki kuma jarumin shirin fim din Kannywood, Shu’aibu Ahmed Abbas, wanda kowa ya fi sani da Lilin Baba ya bayyana wa duniya cewa yanzu haka shirye-shiryen auren sa da jaruma Ummi Rahab ya kankama, Aminiya ta ruwaito.

Ina taya ki murnar zagayowar ranar haihuwar ki abar kauna ta, Ummi Rahab. Lallai kin kasance mutumiyar kirki ma’abociya zuciyar zinare.

“Ina tura miki sakon taya murnar zagayowar ranar da aka haife ki a daidai ranar da ki ka kara wata shekarar a rayuwar ki.

“Ina fatan yau za ta zama ranar murna a gare ki tare da farin ciki. Ina jin dadin ganin yadda kika samu ci gaba a rayuwar ki. Ina fatan Allah ya albarkaci rayuwar ki.”

Can a karshen wallafar tasa sai ya ce:

“Na kusa yin Wuf da ke in sha Allah!”

A karkashin wallafar, jarumar ta nuna jin dadin ta dangane da wallafar ta shi inda ta yi masa tsokaci.

Kamar yadda ta yi masa martani inda ta ce:

“Ina mika godiya ta abin kauna ta. Lallai kai ne a gaba cikin jerin mutane, mijina na nan gaba. Na kosa in ga ranar. Allah ya nuna mana.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Daily Trust

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe