Malamin makaranta ya kwashe albashin sa wajen yin gyaran makarantar da yake koyarwa

  • Post author:
  • Reading time:4 mins read
You are currently viewing Malamin makaranta ya kwashe albashin sa wajen yin gyaran makarantar da yake koyarwa

Shugaban makarantar firamaren Kwasi Nyarko Presbyterian Primary School, Richard Boakye Marfo, yayi amfani da albashin sa wajen yin sabon fenti a makarantar domin ƙarawa makarantar kyau. Legit.ng ta rahoto

Makarantar wacce take a gundumar Upper West Akim District a cikin yankin gabashi, tana goga kafaɗa tsakanin ta da sauran makarantun yankin.

Ya bayyana dalilin yin gyaran

Marfo ya shaida wa GBC News cewa ya fara wannan aikin ne domin ganin makarantar ta ƙara kyau yadda zata samun ƙarin yawan ɗalibai. 

Wannan shine karo na biyu da malamin makarantar na ƙasar Ghana yayi irin wannan abin a zo a gani da dukiyar sa tun lokacin da ya zama shugaban makarantar a shekarar 2019. Ya bayyana cewa hukumomi ba su da masaniyar cewa ya gudanar da wannan aikin

Marfo ya bayyana cewa gabaɗaya aikin, wanda ya haɗa da gyaran kofar shiga makarantar da fentin makarantar sau biyu, sun lashe kuɗi kimanin GHc14,000 (N825,859.23).

Yayi wani babban roƙo

Ya roƙi gwamnati, ƙungiyoyi da masu hannu da shuni su kawo musu agajin kujerun zama.

Ya kuma ƙara yin roƙon ganin an samar wa da makarantar wajen koyon kwamfuta domin ƙara haɓɓaka koyarwa.

Ciwon ‘ya mace: Lynda Iroegbu ta bude wa wata mata ai yara 3 shago domin ta samu na dogaro da kai

Lynda Iroegbu a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, ta bayyana yadda ta cire wata mata a ciki kunci a ranar bikin masoya ta duniya, ta hadu da matar ne a ranar 21 ga watan Disamba 2021. Lynda ta bayyana cewa matar ta kasance mahaifiya ga yara biyar da su ke fama da kalubalen rayuwa.A cikin wannan halin kuncin ne har ta rasa yaranta 2.

Ta ce wa matar duk shagon nata ne

‘Yar sana’ar da ta ke lallabawa wasu ‘yan daba suka far mata. Saboda lynda ta rage wa matan radadin rashi, sai ta bude mata shagon siyar da kaya.
Lynda ta bayyana wa matar cewa da kwantenan da kayan ciki duk mallakin ta ne, ta ba ta. Ta kuma kara da addu’a cewa: 

Allah ya nisanta wannan mata daga talauci ta kuma yi mata fatan Allah ya albarkaci kasuwancinta.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: in[email protected]

Rubuta Sharhi