BASAJAN AIKI: Bayan wata uku 3, wata mata ta gano ‘yar aikin da ta dauka ba mace bace, gardi ne 

You are currently viewing BASAJAN AIKI: Bayan wata uku 3, wata mata ta gano ‘yar aikin da ta dauka ba mace bace, gardi ne 
BASAJAN AIKI: Bayan wata uku 3, wata mata ta gano yar aikin da ta dauka ba mace bace namiji ne 

Wata mata ‘yar Nageriyar ta dauki wata ‘yar aiki, bayan wata uku sai ta gane ashe burum-burum ‘yar aikin tayi mata. 
Matar ta gano cewa ‘yar aikin dai ba mace bace namiji ne inda ta kunyata shi a cikin bidiyon da ya dinga kewayawa a kafafen sada zumuntar zamani.

Anyi ta samun ra’ayoyi mabanbanta juna lokacin da bidiyon dan basajan aikin ya yadu, inda mutumin ya zamo abin ya taba shi sosai. 

Kaddara cewa ku dauki yar aiki mace, bayan wani lokaci kuma ku gano cewa wannan ‘yar aikin ba mace bace namiji ne. Wannan shi ne abin da ya faru da wata magidanciya. 

Matar wacce babu wani takamaiman bayani a kan wacece ita, ta ga abinda ta kasa yarda da shi, cewa mai aikin gidanta ba mace bace namiji ne. 

aiki
BASAJAN AIKI: Bayan wata uku 3, wata mata ta gano ‘yar aikin da ta dauka ba mace bace, gardi ne 

Lamarin wanda @ourtalkroom ne ya yada bidiyon sa, yace matar ba ta gane cewa ‘yar aikin ba mace bace namiji ne, sai bayan watanni uku. 

An kunyata sojan gonar dan aikin

A bidiyon da aka yada, dan aikin yana kasa ne daga shi sai rigar mama ta mata da kuma wandon jins na mata, kana kuma akwai gashin doki a kansa. 
Mayaudarin dan akin dai an gan shi daga baya an saka shi a mota, wanda ko tantama babu cewa ofishin ‘yan sanda za’a mika shi. 

Wani zai iya cewa, ta yaya mutum namiji zai yi basaja a matsayin mace amma a ce har sai bayan wata uku za a gano shi, kai to menene ma ya janyo aka gano shi. 

Mabanbantan sharhi a kan lamarin dan aikin

bonny_noni yace :

” A kalla dai ba sata yayi ba, ko wani abin assha, ko tsafi, kawai mutum yana san kudi kuma ya sami aiki” 

@laureldoll_ @laureldoll_  yace :

” Mai yiwuwa mutumin yana ta neman aikin da zai yi domin ya rayu, sannan kuma zai iya yiwuwa ayyukan da yake gani duk na mata ne. Sannan kuma bai fa yi komai wanda ba daidai ba ne ga jama’a. “

@zayne_ryker yace:

  “Amma idan har zai boye kama dan ya nemi aiki, ina nufin bai fa yi wani abu na ba daidai ba, tsawon wata uku, bai yi yunkurin cutar da ke ba ta kowanne hali, saboda haka ba na ganin ya cancanci irin wannan muzantawa ” 

@absolut_shuga yace :

” Abu guda biyu ne a nan, imma dai aiki yake nema, sai ya boye kama a matsayin budurwa, ko kuma, yana da wata boyayyar manufa”.

Mai digiri ya ajiye aikin banki ya koma sayar da burodi a titi

Wani ma’aikacin bankin Zenith mai suna Ali Dahiru, ya ajiye aikin bankin ya koma sayar da burodi, ya ce wannan shawara da ya yanke ta zame masa alkhairi sosai.

Dahiru, wanda yake da takardun HND, ya kammala karatu a Polytechnic dake Kaduna, a fannin tattalin arziki, ya sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa yana sayar da burodi akan titiunan Kaduna, kuma yana alfahari da wannan aiki na sa.

Bayan na kammala karatuna, na fara aiki da bankin Zenith na tsawon shekara shida, kafin daga baya na ajiye aikin na fara sayar da burodi.

Da yake bayyana yadda ya fara sha’awar sayar da burodi, Dahiru ya ce wani mutumi da yake kai musu burodi banki suna saya, shine ya sanya masa sha’awar sana’ar.

2023: IBB, Obasanjo, Saraki, da Secondus sun yi ganawar sirri

A lokacin da nake hutu ne na yanke shawarar magana da mai sayar da burodin a bankin, inda na nuna masa ina sha’awar sana’ar.

Na gano cewa ribar da yake samu a wata wajen sayar da burodi tafi albashin da nake dauka a wata a banki.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: NAN

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Rubuta Sharhi