Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya karanto ayoyin Alkur’ani mai girma a wurin wani taro

You are currently viewing Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya karanto ayoyin Alkur’ani mai girma a wurin wani taro
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya karanto ayoyin Alkur'ani mai girma a wurin wani taro

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya karanta wasu ayoyi Al’kur’ani a lokacin da yake bayani a garin bikin hadin kan tarayyar Rasha. 
A fadar kafafen yada labarai na kasar Rashan, Vladimir Putin din ya yayi jawabi ga taron hadin kan tarayyar Rashar, wanda shugabannin bangarorin yankuna  da dama na tarayyar kamar, Musulmai, Yahudawa, Kiristoci da kuma Hindu suka halarta. 
Da yake magana a taron, Vladimir Putin din ya janyo ayoyin Al’kur’ani mai girma a cikin sura ta 23 Shura aya ta 42: wadda take cewa :

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya karanto ayoyin Alkur'ani mai girma a wurin wani taro
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya karanto ayoyin Alkur’ani mai girma a wurin wani taro

” Wannan shine kyakkyawan albishir da Allah yake yi wa bayinsa da suka yi imani, kuma suka yi aiki na gari. Kace : Ni bana tambayar ku Lada sai dai Soyayyar iyalan Annabi. Kuma Za mu da mai kyau ga duk wanda, Lallai Allah mai gafara ne kuma mai godiya ” 

Bugu da kari kuma, Vladimir Putin, ya sake janyo wata aya a cikin sura ta 128 Nahli aya ta 16, wadda take cewa : 

” Lallai Allah yana tare da suke shiyarwa (ga barin hanyar barna )  da kuma wadanda suke aikata kyakkyawa (ga mutane ).”

Shugaba Vladimir Putin din, ya janyo wadannan ayoyi ne domin yayi bayani a kan kyakkyawan ma’amala, kawance, da kuma ladan wanda yayi kyakkyawan aiki a rayuwar sa. 

Bayan haka kuma, ya yanko wadansu sadarori a cikin Attaura, da Bible domin ya yi jawabi ga Yahudawa da Kiristoci. 
A karshe, ya kuma caccaki kasar Faransa, saboda yadda take wulakanta lamarin musulunci

Ba za mu yadda a cigaba da cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW) ba – Shugaban kasar Rasha Putin

A cewar shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW) bai nuni da cewa hakan ‘yancin dan adam ne. Kamar yadda Tashar CRUX ta YouTube ta wallafa a shafinta.

Da yake bayani a wajen taron manema labarai da ya gabatar a ranar Alhamis, Putin ya ce cin zarafin Annabi Muhammad (SAW), ya sabawa ‘yancin addini, kuma ya sabawa mutanen da suke bin addinin Musulunci.

Shugaba Putin ya ce masu tsattsauran ra’ayi na addini sune suke jawo irin wannan tashin-tashina, inda ya bayar da misali da gidan jaridar Charlie Hebdo dake birnin Paris, kan yadda aka dinga kai musu hari bayan sun wallafa hoton batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Islamic Information

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Rubuta Sharhi