24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

NSCDC ta sada yaro mai shekaru 13 da mahaifiyar sa bayan rabuwar su da shekaru 11

LabaraiNSCDC ta sada yaro mai shekaru 13 da mahaifiyar sa bayan rabuwar su da shekaru 11

Sashin kula da zaman lafiya (PCM) na hukumar tsaron farar hula ta Najeriya (NSCDC) reshen Jihar Jigawa ta sada wani yaro dan shekara 13 mai suna Auwal Musa Adam, da mahaifiyar sa, Aisha Hassan Kachako ta anguwar Nasarawa a Kachako da ke Jihar Kano, bayan shekara sha daya da rabuwar su.

Kakakin hukumar, CSC Adamu Shehu, wanda ya bayyana hakan a wata takarda ya ce, an sada mahaifiyar da danta a ranar Alhamis, 3 ga watan Maris, LIB ta ruwaito.

yaro da mamansa
NSCDC ta sada yaro mai shekaru 13 da mahaifiyar sa bayan rabuwar su da shekaru 11

“Mahaifiyar (Aisha Hassan), ta shigar da korafi ga hukumar a ranar 17 ga watan Fabrairun 2022 cewa, tsohon mijinta, Malam Musa Mamuda ya kai yaron ta Jamhuriyar Niger, inda ta zarge shi da safarar yaron bayan rabuwar aurensu,” kamar yadda takardar tazo.

“A lokacin da aka amshi korafin, sashin kula da zaman lafiya na hukumar ya gayyaci mahaifin yaron, Musa Mamuda. Yayin da bincike ya nuna yadda tsohon mijin nata ya tafi da yaron da ake rikici akai, inda ya kai wa ‘yar uwar mahaifiyar sa.

“Hukumar ta umarci mahaifin da ya nemo yaron cikin makwanni biyu ko kuma ya fuskanci fushin shari’a. An shirya yadda za’a maido da yaron, daga bisani aka sada shi da mahaifiyarsa bayan shekara sha daya da rabuwar su.

“Mahaifiyar yaron ta shiga cikin farin ciki maras misaltuwa a lokacin da tayi tozali da yaron nata. Sai dai, yaron bai iya tunawa da ita ba duba da yadda aka raba shi da ita, tun yana dan shekara biyu.

“Mahaifin ya bayar da labarin yadda bayan rabuwar su, ya kai yaron wurin ‘yar uwar mahaifiyar sa a Jamhuriyar Nijar, saboda yadda ya zargi tsohuwar matar sa da karancin tarbiyya.

” Sashin PCM na kokarin ganin ta sulhunta iyayen, don ganin wanda ya cancanci kula da yaron ba tare da haifar da matsala da lafiyar sa ba. Idan hakan bai yuwu ba, za’a mayar da lamarin zuwa kotu.”

Yaro dan shekara 15 da ya fara sana’ar sayar da riguna tun yana dan shekara 12 ya samu ribar naira miliyan 913 a shekara daya

A lokacin bikin zagayowar ranar haihuwar sa karo na 12, Trey Brown yana da ƙwaƙwalwa wacce ba kasafai ake samun ta a wajen yara masu shekarun sa ba.

Hikimar siye, gyarawa da kuma sayar da riguna ta zo masa. Ya yanke shawarar yin amfani da N73,830 ɗin da ya samu wajen bikin zagayowar ranar haihuwar sa wajen siye sannan ya gyara riguna kafin sayar da su ga mutanen yankin sa. Legit.ng ta rahoto.

Brown ya shaida wa shirin ABC mai suna Shark Tank cewa rigunan sa suna ƙarewa da wuri a kasuwa.

Kamfanin na samar da ƙuɗaɗe sosai

Ya ƙirƙiri kamfanin inda ya sanya masa sunan Spergo. Ya bayyana cewa yanzu haka kamfanin yana kan hanyar samun kuɗin shiga kimanin miliyan 900.

Brown ya fara kafa wannan wannan sana’ar ta sa a farkon shekarar 2018 da taimakon mahaifiyar sa Sherell Peterson, wacce tshouwar mai ɗinki ce kuma yanzu ta ke riƙe da muƙamin babbar mai gudanar da ayyuka ta kamfanin.

Yanzu kamfanin Spergo, yana siyar da kayayyaki irin su safuka, riguna, rigunan sanyi da wanduna waɗanda ke da farashin N48,980, N18,675, N33,200 and N40,670 respectively.

Ya cimma wata yarjejeniyar kasuwanci da wani babban mutum

A farkon fara kamfanin sa, Brown ya cimma yarjejeniyar naira miliyan N124.5 da mai kamfanin FUBU, Daymond John domin mallakar kaso 20 na cikin Spergo.

John ya bayyana cewa akwai alaƙa tsakanin hangen nesan Brown da na shi saboda shi ma lokacin da ya fara kamfanin sa na kayan sawa, mahaifiyar sa ta taka muhimmiyar rawa sosai.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe