Matar aure ta maka mijinta a kotu kan zargin yana cusa mata ’tissue’ a gabanta

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
You are currently viewing Matar aure ta maka mijinta a kotu kan zargin yana cusa mata ’tissue’ a gabanta
Matar aure ta maka mijinta a kotu kan zargin yana cusa mata 'tissue' a gabanta

Wata ma’aikaciyar gwamnati kuma matar aure mai suna Esther Anaagu, a ranar Alhamis ta maka mijinta Emmanule a gaban wata kotu da ke Jikwoyi da ke garin Abuja bisa zargin sa da cusa mata takardar “tissue” a cikin gabanta.

Misis Esther, a cikin takardar karar ta ce: “Mijina yana tura min takadda a gabana bayan ya gama jima’i da ni.

“Wata rana nayi ƙarfin hali na tunkare shi game da abunda ya ke aikatawa. A take a nan ya musanta. Saboda haka, wata rana, sai na dana masa tarko in da na kama shi yana nannade takardar a al’aurarsa kafin ya sadu dani” in ji ta.

Matar aure ta maka mijinta a kotu kan zargin yana cusa mata 'tissue' a gabanta
Matar aure ta maka mijinta a kotu kan zargin yana cusa mata ’tissue’ a gabanta

Matar auren ta ce ta dade tana zargin mijin nata da yunkurin kashe ta.

Wanda ake kara ya musanta zargi

Wanda ake kara mai suna Emmanuel wanda ya kasance direban tasi ne ya musanta zargin da ake masa.
Alkalin kotun, Labaran Gusau, ya shawarci ma’auratan da su yi kokarin ganin sun sasanta kansu ko dan saboda ‘ya’ya dake tsakanin su.

Gusau ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 24 ga watan Maris, domin samun rahoton sasantawa ko kuma cigaba da sauraron karar.

Bidiyo: Yadda tsohon mijina da mahaifiya ta suka dinga lalata na shekaru 15, mata ta koka


Soipan Martha ta bayyana yadda ta taso da burin samun soyyayar mahaifiya, amma hakan bai tabbata ba don mahaifiyarta ta bige da lalata da mijin ta, Legit.ng ta ruwaito.

Yayin da ta cika shekaru biyu da haihuwa, mahaifiyarta ta bar ta karkashin kulawar babbar yayarta, daga bisani ta nufi Saudiyya don neman kudi.
Ta labarta yadda rayuwa ta yi mata dadi bayan tuna cewa zata sadu da mahaifiyar ta.
Bidiyo: Yadda tsohon mijina da mahaifiya ta suka dinga lalata na shekaru 15, mata ta koka
Wata rana, mahaifiyarta koma gida daga kasar Kenya, wanda bayan nan ta mayar da ita makarantar kwana ba tare da wani ya ci gaba da kai mata ziyara ba.

Wannan ya janyo mata kusanci da shugabar makarantar, wacce ta lashi takobin alwashin rike ta tamkar mahaifiyar ta wanda tayi hakan.

Da taimakon kakarta, ta shiga makarantar sakandire bayan kammala firamare, daga nan ta fara aiki har ta hadu da wani mutum inda suka fara soyayya. , inda ta hadu da wani mutum, har suka fara soyayya.

A cewarta:

” Nayi tunanin yana so na da gaskiya saboda irin kulawar da yake ba ni a lokacin.

Sai dai bayan na tare gidansa, matsaloli suka fara aukuwa. Ya lakada min duka a ranar da na koma gidansa sannan ya kwace min sulalla ta.”

Martha ta bayyana cewa duk lokacin da ta bukaci taimako daga mahaifiyar ta, tana kare mijin nata, ta hanyar musantawa.

Ta labarta yadda tsohon mijin nata da mahaifiyarta suka dinga lalata na tsawon shekaru kamar yadda ya fadi a gaban ta kuma mijin bai musanta ba.

“Na yi mamaki akan yadda lamarin ya auku kuma na shiga rudani mai yawa.”

Ta sanar da yadda tsohon mijin ya dirka wa mahaifiyarta ciki daga bisani ya guje ta.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi