Abubuwan da ke ciki
Sahun farko na jirgin da ke ɗauke da ‘yan Najeriyan da su ka maƙale a ƙasar Ukraine ya iso gida Najeriya.
Sun iso gida Najeriya ne daga ƙasar Romania a safiyar ranar Juma’a. Jaridar PUNCH ta rahoto
Hukumomi sun tabbatar da isowar su
Shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya da ke zama a ƙasashen waje, Abike Dabiri Erewa, ta tabbatar da hakan a wata wallafa da tayi a shafin Twitter.

Rukunin farko na ‘yan Najeriya daga Ukraine ya iso filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja, daga Romania da misalin ƙarfe bakwai da mintuna goma (7:10am) na safiya.
A ranar Laraba da ta gabata ne gwamnatin taryya ta amince da dala miliyan 8.5 domin gaggauta kwaso yan Najeriya 5,000 da ke makale a ƙasar Ukraine a sakamakon yakin da ƙasar Rasha ta ƙaddamar akan ƙasar Ukraine.
An kwaso jimillar mutane 411, waɗanda su ka haɗa sa ma’aikatan ofishin jakadancin Najeriya a ƙasar Ukraine da kuma sauran ‘yan Najeriya.
Elon Musk da Jeff Bezos sun tafka asarar tiriliyan N7.4 a rana ɗaya a dalilin rikicin Rasha da Ukraine
Elon Musk da Jeff Bezos sun tafka asarar tiriliyan N7.4 a rana ɗaya biyo bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin ƙasashen Rasha da Ukraine.
Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk, tattalin arziƙin sa ya dawo dala biliyan $199 ($199 billion) bayan ya tafka asarar dala biliyan $13 ($13 billion).
Jeff Bezos, mutum na biyu cikin jerin masu arziƙin duniya kuma mai kamfanin Amazon, ya tafka asarar dala biliyan $5.41 inda tattalin arziƙin sa ya dawo dala biliyan $169
Faɗuwar kadarorin su ta zo ne bayan an sanar da cewa sojojin Rasha sun fara tada bama bamai a wasu yankunan ƙasar Ukraine, wanda hakan ya sanya ɗar-ɗar a cikin kasuwanni. Ƙasuwar crypto tayi ƙasa sosai a safiyar Alhamis 24 ga watan Fabrairun 2022. Farashin ɗanyen man fetur yayi tashin gwauron zabi zuwa $100 kan kowace ganga.
An sayar da ɗanyen mai kan farashin $95 kowace ganga a wasu lokuta yayin hada-hadar kasuwanci a ranar Alhamis 22 ga watan Fabrairun 2022.
An sayar da shiyar kamfanin Tesla akan dala $764.04, inda ta ragu da kaso 7 kan yadda aka sayar da ita a kasuwar baya. Sai dai darajarta ta ƙaru inda ta samu ƙarin kaso 2.91% inda aka sayar da ita kan dala $787.27
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Facebook Page
Twitter Page
Telegram Channel
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]