Abubuwan da ke ciki
Ministan ƙwadago Dr Chris Ngige ya bayyana cewa gwamnatin tarayya bata da kuɗaɗen da zata iya cika alƙawarin da ta yiwa ƙungiyar malama jami’a ta ƙasa watau ASUU.
Gwamnati na son sake duba alƙawarin ta da ASUU
Ngige ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na duba yiwuwar sake tattauna alƙawarin da ke tsakanin ta ASUU domin ganin an kawo ƙarshen yajin aikin da malaman jami’ar ke yi. Jaridar PUNCH ta rahoto
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani shiri mai suna (Politics Today) na tashar talabijin ta Channels TV ranar Alhamis.
Da aka tambaye shi ko zuwa yaushe ake sa ran kawo ƙarshen taƙaddamar sai ya kada baki yace:
Ina fatan cewa ASUU za suyi abinda ya dace wajen tuntubar mambobin su akan abubuwan da mu ka sake tattaunawa sati biyun da su ka wuce. Abu na farko shine, maganar alawus, mun yarda cewa za mu ba hukumar jami’o’i ta ƙasa (NUC) damar yin amfani da tsohon tsarin da tayi amfani da shi a 2021, watau na kaso 10.8
Muna son su gaggauta sake yin amfani da wannan tsarin sannan su kawo mana abinda zamu biya a 2022. Kowane ɓangare ya gamsu da wannan.
Dangane da sakin kuɗi naira tiriliyan N1.3 domin gyaran jami’o’i tsakanin 2013 zuwa 2018, inda aka bayar da biliyan N200bn a shekarar 2013 amma aka bayar da biliyan N70bn kawai a cikin shekaru 7 da su ka gabata, ministan ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ce tayi alƙawarin bada N1.3trn. A cewar sa a lokacin ana sayar da gangar ɗanyen mai a kan farashin dala $100 zuwa dala $120, lokacin da gwamnati ke samun kuɗaɗen shiga sosai.
Ba zamu iya biya ba
Gwamnatin yanzu ta ce ‘ba mu da ƙuɗin da zamu iya biya.’ Wannan alƙawari ne wanda aka yi tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017. Ya kuma ƙara da cewa har yanzu gwamnati ba ta da ƙuɗaɗen da za ta iya cika wannan alƙawarin.
Ngige ya bayyana cewa gwamnati yanzu tana neman sake duba matsayar da ta cimma tsakanin ta ASUU.
Mun shirya tsaf domin yajin gaggawa, Cewar Kungiyar ASUU
Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), ta ce ta shirya tsaf don ayyana yajin aikin sai baba ta gani nan babu dadewa.
Da yake fitowa daga taron majalisar gudanarwa a ranar Laraba a Abuja, shugaban fannin gudanarwa na kungiyar ASUU shiyyar Abuja, Dakta Salahu Mohammed Lawal, ya ce kungiyar ba za ta shiga wata sabuwar yarjejeniya ba, ko wata sabuwar tattaunawa ko kuma sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna da aiki tare da gwamnatin tarayya.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]
Gaskiyar mgn amatsayinmu na dalibai muna Kira ga gwamnatin tarayya da tagaggauta yima malaman Jami a adalci domin cigaban goban mu Yan Nigeria