Amfanin dabino guda 5 ga ɗan adam masu ban mamaki

You are currently viewing Amfanin dabino guda 5 ga ɗan adam masu ban mamaki
Amfanin dabino guda 5 ga ɗan adam masu ban mamaki

Dabino wani ɗan itace ne mai launin ruwan ƙasa, mai taunuwa, Yana daga cikin ‘ya’yan itatuwa masu daɗi waɗanda aka samo daga a Phoenix dactylifera.

Ana sayar da dabino ne a busasshiyar yanayi; ya shahara a cikin Larabawa da kasashen Afirka. Busassun dabino ya kan mallaki fata mai yakuni, kuma ana kiransu da sunan ‘dabino’ a sassan arewacin Najeriya.

Dabino
Amfanin dabino guda 5 ga ɗan adam masu ban mamaki

Ga amfanin cin dabino ga ɗan adam:

Ya ƙunshi antioxidants

Ya’yan dabino suna ƙunshe da antioxidants masu yawa waɗanda ke taimakawa rage haɗarin cututtuka da yawa. Dabino ya ƙunshi flavonoids da phenolic acid, waɗanda ke da sinadarai na hana kumburin ƙwayar cuta wanda ke taimakawa wajen rage haɗarin kamuwa da ciwon sukari da cututtukan zuciya.

Yana Sauƙaƙa Naƙuda

Bincike ya nuna cewa dabino na taimakawa wajen inganta haihuwa a cikin ‘yan makonnin da suka gabata na yin ciki. Ƙwayoyin suna haɓaka faɗuwar mahaifa, wanda hakan ke rage lokacin naƙuda na mace mai ciki. Ya’yan dabino sun ƙunshi sinadarin tannin da sikari na halitta, waɗanda ke taimakawa sauƙaƙa ƙanƙancewa yayin da suke riƙe da mafi kyawun matakin kuzari.

Mallakar Sinadarin Zaƙi na asali

Ya’yan dabino sun ƙunshi fructose wani haɗaɗɗen sukari na halitta da ake samu a cikin ‘ya’yan itatuwa. Dabino yana da ɗanɗano mai daɗi, sannan kuma yana da wadataccen fiber da sinadarai masu yawa; a sakamakon haka, ana iya amfani da shi a matsayin lafiyayyen sukari na al’ada. Kuna iya haɗa shi a cikin garri, custard, ko hatsi.

Inganta Lafiyar Ƙashi

Ya’yan dabino babban tushen ma’adanai ne kamar calcium, magnesium, phosphorous; Waɗannan zasu iya taimakawa wajen rage haɗarin cututtukan da ke da alaƙa da kashi kamar osteoporosis (wannan shi ne raunin ƙasusuwan, wanda ke haifar da raguwa).

Yana Inganta Kuzarin Maza

‘Ya’yan dabino sun ƙunshi sinadarai masu amfani kamar estradiol da flavonoids, waɗanda ke haɓaka ƙidayar maniyyi kuma suna haɓaka haihuwa da kuzarin ga maza.

Yana inganta lafiyar kwakwalwa Bincike ya nuna cewa dabino na taimakawa wajen rage ci gaban cutar Alzheimer a cikin tsofaffi. Wani abu mai kyau game da dabino shine ana iya shigar da shi cikin sauƙi a cikin abincin mutum ba tare da canza abincin ku na yau da kullun ba.

Za a dawo da shan ruwa a Masallacin Annabi cikin watan Ramadana bayan shafe shekara 2 da dainawa saboda COVID

A yayin da watan Ramadana mai albarka ke cigaba da karatowa, hukumar kula da harkokin Masallacin Annabi dake Madinah, ta bayyana kudurinta na dawo da shan ruwa a cikin Masallacin bayan shafe shekara biyu ba a yi ba sakamakon annobar COVID-19.

Don ganin an kare lafiya da rayukan al’umma, hukumar ta dakatar da shan ruwa a Masallacin na Annabi tun a ranar 24 ga watan Afrilun shekarar 2020, wanda ya yi daidai da shekarar 1441 ta Musulunci.

Hukumar lura da harkokin Masallacin za ta dawo da shan ruwa a cikin Masallacin cikin watan Ramadana dake karatowa.

Sai dai kuma hukumar ta bayyana cewa iya wadanda aka bawa lasisin yin hakan ne kawai za su samu damar shiga domin su gabatar da ibada da kuma buda baki.

“Sakamakon duba da muka yi dangane da matsalar annobar COVID-19, za mu duba iya yawan mutanen da za su iya shiga su ci abinci a kowacce Sofra.

Hukumar ta bayyana wadanda za su dinga kawo kayan shan ruwan za su kulla yarjejeniya da wuraren dafa abinci da za su dinga kai wa, sannan kuma kowacce Sofra mutane biyar kawai za a bari su zauna su ci abinci a wajen, don ganin an bi dokar hana yaduwar annobar COVID-19.

Bayan haka kuma, dokar cin abinci ta bayyana cewa kowa zai zauna a bangare daya ne zai fuskanci alqibla. Daga ranar 2 ga watan Fabrairun shekarar 2022, hukumar za ta fara aikawa da mutanen da suke da lasisin bayar da abincin sakonni.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi