Mutanen ƙabilar Kambari: Ɗaya daga cikin ƙabilun Najeriya da suke rayuwa tsirara

You are currently viewing Mutanen ƙabilar Kambari: Ɗaya daga cikin ƙabilun Najeriya da suke rayuwa tsirara
Mutanen ƙabilar Kambari: Ɗaya daga cikin ƙabilun Najeriya da suke rayuwa tsirara

Ƙabilar Kambari tsohuwar al’ummar karkara ce a jihar Neja, ɗaya daga cikin ‘yan tsiraici da har yanzu suke rayuwa cikin tsiraici.

Mutanen Kambari suna alfahari da kasancewa masu cin gashin kansu daga gwamnati gwargwadon iko.

Kambari al’umma ce mai nisa a garin Birnin Amina da ke karamar hukumar Rijau a jihar Neja inda mutane ke yawo tsirara. Ƙabila ce da aka manta da su kuma sun gamsu da salon rayuwarsu mai sauƙi da nuna rashin goyon bayan su ga gwamnati game da cigaban al’umma mai ɗorewa.

Kambari tribe
Mutanen ƙabilar Kambari: Ɗaya daga cikin ƙabilun Najeriya da suke rayuwa tsirara

Hanyar rayuwar kabilar Kambari


Kambari ba sa jin Turanci ko Hausa, sai dai suna magana da harshen Kambari. Suna zama a cikin ƙananan yankunansu kuma suna hulɗa da wasu kawai lokacin da za su je gona da kasuwa. Tsiraici a matsayin al’ada kakanninsu ne suka ba su kuma wani ɓangare ne na su da ba sa son barin sa. Sai dai kuma idan suka je kasuwa don sayar da amfanin gonakinsu, matan da mazan dukansu kan rufe rabin jikinsu daga ƙasa da zani. Suna amfani da jakuna a matsayin hanyar sufuri ga masu noma da makiyaya.

Aure a kabilar Kambari


A garin Kambari dai ana gudanar da ɗaurin aure ta hanyar yanka akuyoyi da shanu domin abinci yayin da iyayen amarya ke dafa wa ango abinci. Da zarar an ci abinci sai a daura auren. A cewar shugaban al’ummar, abin da ke jan hankalin maza ba wai tsiraicin matan ba ne, sai dai yadda suke yi wa gashin kansu ado da kyawawan halaye da kuma irin jarfa da ‘yan matan suke yi.

Addinin mutane Kambari


Mutanen Kambari ba Kiristoci ba ne ko Musulmai ba kamar yawancin Arewacin Najeriya. A maimakon haka, su arna ne masu bautar wani abin bautar da ake kira Magiro. Sun kuma yi imani mai ƙarfi da sihiri.

Tattalin Arzikin Kambari


A wani yanki na karamar hukumar Rijua, mutanen Kambari suna noma kaso mai yawa na amfanin gona da ɗaukacin al’ummar yankin ke ci. Mafi shaharar amfanin gona da ake nomawa sune masara, gero, gyada, wake, da shinkafa. Kusan dukkan mutanen yankin suna ajiye kaji da awaki don nama yayin da masu arziki ke da shanu.

‘Yan bindiga sun kai sabon farmaki a ƙauyukan jihar Neja, sun halaka mutum 3

Hukumar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da halaka mutane uku da ‘yan bindiga su ka yi a ƙauyukan Ebbo da Ndagbeji na ƙaramar hukumar Lavun a jihar. Jaridar Daily Trust ta rahoto

Hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Neja, Mr Monday Kuryas, ya tabbatar da aukuwar lamarin yayin wata zantawa da News Agency of Nigeria (NAN) babban birnin jihar Minna ranar Lahadi.

Mr Kuryas ya bayyana cewa lamarin ya auku ne ranar Lahadi da safe lokacin da ‘yan bindiga su ka afkawa ƙauyukan.aid
A cewar sa, an tura jami’an ‘yan sanda na musamman da sojoji zuwa yankin inda tuni su ka fara farautar ‘yan bindigan.

Mu na kira ga mazaunan yankin da su taimaka wajen bada sahihan bayanai waɗanda za su taimaka wajen zaƙulo ɓata garin da su ke a cikin su.

A cewar kwamishinan ‘yan sandan

Jihar na fama da matsalar ‘yan bindiga

Jihar Neja tana ɗaya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya waɗanda su ke cigaba da fama da matsalar ‘yan bindiga. ‘Yan bindigan sun yi ƙaurin suna wajen kai hare-jare ga mutanen da ba suji ba ba su gani.

Mutane da dama sun rasa rayukan su da dukiyoyin sun tun lokacin da rikicin ‘yan bindiga ya ɓarke a yankunan na Arewacin Najeriya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

This Post Has One Comment

  1. Abdullahi sale

    Poor research this is Eurocentric view ba akwai akan KAMBARI ba but must African people ama me yasa Ku bazakuje kubincika da kanku ba to waga labari karya ne ayanzu anti gonna Bakambare anti minister Bakambare nima Bakambare kuma nayi rubutu sosai game da tarihin KAMBARI da kunce kabilar KAMBARI ada can baya ama nunawa dakukayi kamar har yanzu to yanuna jahilcinku game da abinda kuka rubuta daga Rijau, Magama, mashegu , Borgu, kontagora a jihar Niger har zuwa Yawuri da Ngaski a jihar kebbi kai hada da Kaima local government a jihar kwara duk wurarennan da na lisafa akwai KAMBARI awurin sosai ba inda banjeba don nemo tarihi da rayuwar KAMBARI ama ba inda zaka samu Bakambare zindir kamar yada kuke nufi saboda haka kabar rubuta labari da kai nayi unfani da zuciya wurin fyede gaskiya

Rubuta Sharhi