- Wata budurwa yar shekara 70, mai suna Genevieve ta bayyana muradin ta na auren saurayi mai shekaru 21
- Matar, wacce bata taba barin gidan ta ba, ta bayyana yadda bata taba saurayi ba, kuma batasan dadin soyayya ba
- Genevieve ta dau tsawon shekaru tana rayuwa cikin yanayi mara dadi, saboda matsalar lafiyar kafa da take fama dashi
Wata budurwa ‘yar shekara 70, mai suna Genevieve, wacce bata taba kusantar wani ba, duk ba ita ta zabi hakan ba; sai dai a cewarta haka rayuwa tayi da ita, Legit.ng ta ruwaito.
Genevieve tana fama da matsalar gurgunta, hakan ya tilasta mata rarrafe saboda bazata iya amfani da kafar ta ba; bata taba tafiya ba a rayuwarta.
Kuma bata taba saurayi ba ko samun ilimi ingantacce.

Yayin zantawa da Afrimax, gurguwar budurwa ta ce, an haifeta a shekarar 1952.
Sai dai, a lokacin da iyayen ta suka farga diyar tasu bata iya tafiya, cigaba da rarrafe tayi. Sun yi zaton lamarin zai canza idan ta kara tasawa, amma hakan bai kasance ba.
Budurwar ta bayyana yadda tayi fama da cuta a lokacin da tana yarinya, wanda hakan ne ya shafi kafarta, kuma yasa ta zama lalura ga iyayenta.
Iyayen Genevieve basu tura ta makaranta ba, saboda basu da kudin siya ma ta kujerar guragu, sannan ba za su iya kai ta da dawo da ita kullum ba.
Baya ga rashin samun damar neman ilimi, halin da take ciki ya hana ta samun masoyi.
Saurayi ya halaka budurwarsa, ya kira ‘yan uwanta ya sanar musu sannan ya cika wandonsa da isa
Ana zargin wani saurayi da kashe budurwarsa a Abuja, ya kuma sanar da ‘yan uwanta cewa “su zo su dauki gawar ta”.
A watan Mayun 2021, kuma ya shiga cikin watan Agusta na wannan shekarar, an bayyana cewa wanda ake zargin ya koma gidan marigayiyar ne saboda ba shi da aikin yi kuma ba shi da wurin kwana.
An ruwaito cewa Evelyn ta sauke nauyin kudi na Ugochukwu, wanda aka ce ya yi mata fyade ko kadan.
Ta yi shirin ficewa daga falon saboda cin zarafinta da yake yi. Sai dai kuma a ranar Asabar, 19 ga watan Fabreru, sun samu saɓani inda ya shaƙe ta har lahira ya gudu.
“Bayan ya gudu zuwa wani wurin ɓuya, Ugochukwu ya kira mahaifin Evelyn a kauyen yana tsoratar da shi game da mutuwar Evelyn, cewa ya zo ya ɗauki gawar ‘yarsa.
“Ya kuma kira wani surikin sa ya ce masa haka. Uban ne ya kira daga ƙauye ya sanar da ‘yan uwa a Abuja. Haka labarin ya kasance.” Wata majiya ta ce.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan sanda sun gano gawar ta a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu.
Abokan marigayiyar sun yi ta yadawa a shafukan sada zumunta na yanar gizo suna jimamin rasuwar ta.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com