Yadda wani mutum ya sauya siffar motarsa ta marsandi zuwa gadon baccinsa

  • Post author:
  • Reading time:7 mins read
You are currently viewing Yadda wani mutum ya sauya siffar motarsa ta marsandi zuwa gadon baccinsa
Yadda wani mutum ya sauya siffar motarsa ta marsandi zuwa gadon baccinsa

Idan ka samu damar yin bacci a kan mota kirar marsandi a matsayin gadon bacci ,mutane da yawa sun yi imanin cewa mutum zai yi mafarki mai dadi.

Wani mutum bayyana wa duniya irin gadon da yake kwana a kai kowanne dare sai dai abun mamaki motar Marsandi ce, wacce aka kera masa don shi daya. Motar ta kasance mai launin shuɗi tare da bonnet da fitilolin mota duk an yi amfani da su wurin kera gadon. Sannan gadon yana da tayoyi a kasa wadanda suke rike da shi.

Benz
Yadda wani mutum ya sauya siffar motarsa ta marsandi zuwa gadon baccinsa

Gado ya kayatar, bacci zai yi dadi

Yana matukar son gadon saboda haka ne ya sa shi nuna wa duniya wanda hakan yasa jama’a da dama tofa albarkacin bakin su.

Tsokacin jama’a

@tekk44 ya ce: “Amma dai wannan gadon na yara ne ko?”

@shahriyar.hsm ya ce: “Kawai ina hango irin faduwan da mutum zai yi idan yana bacci.”

@scotch.and.shade ya ce :”Ai wannan rayuwar ciwon baya ne kawai.”

@santram8368 ya ce: “Sai an sha wahala ake yin nasara.”

@anubhav._.10 ya ce : “Abin ban mamaki yadda wasu ke son mayar da motocinsu kamar gadonsu gidajen su kuma kamar motar su”.

A wani labarin na daban, wani dan Najeriya yayi amfani da boot din mota kirar Mercedes ya maidashi teburin ofishin sa.
Teburin da aka ƙera shi irin yadda mutumin yake so yana da fitilun birki waɗanda ke aiki suna haska wa. Lokacin da ya yada bidiyon a shafin Instagram, mutumin ya bayyana cewa teburin yana sa shi ya daɗe yana aiki a ofishin sa.

Idan nasamu dama zan koyar da mutane baiwar kere-kere da Allah yayi mini, cewar dattijon da ya kirkiri murhu mai amfani da ruwa

Duk da cewa bai taba shiga aji ba, wani dattijo mai shekaru 67 daga jihar Gombe mai suna Hadi Usman ya iya kirkiro wasu abubuwa masu matukar ban mamaki da suka hada da murhu mai amfani da ruwa wajen dafa abinci.martanin mutane

Kabiru ikalu yace:

Abun birgewa game da wannan mutumi shi ne, yanda ya bayyanar da abun da ya kirkira domin ganin al’umma sun amfana. Ko shakka babu shi bai da son kai kamar sauran mutane. Allah Ya saka masa da yalwar arziki saboda kyakkyawar zuciyarsa.”

Segun Akinbode ya ce:

Amma me ke damun gwamnatinmu???? Ya kamata ace gwamnati ta hada kai da wannan mutumi domin ganin ankera wadanan abubuwa da yawa hakika muna bukatar mu farka mu fuskanci abun da zai haifar mana da da mai ido, Allah ya halici yan baiwa da abubuwa a kasarnan.

Harin NDA: Masu kula da na’urori bacci suke lokacin da aka kai harin – Majiya

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa jami’an dake kula da na’urorin daukar hoto (CCTV) a makarantar horar da sojojin (NDA) bacci suke yi a lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin a ranar Talata 24 ga watan Agusta.

Majiyoyin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun lababa ta wani bangare na makarantar da babu katanga a wajen suka shiga ciki.

Daya daga cikin majiyoyin ya ce:

A cikin tsakar dare ne, kuma jami’an dake aikin lura da na’urorin kyamarar CCTV suna bacci. Da badan haka ba da sun sanar da mutane an yi maganin abun.

Rahoton ya bayyana cewa hukumar makarantar za ta dauki mataki akan wasu daga cikin jami’an sojojin da suka kasa tsare yankin makarantar.

Wata sabuwa: Kotu ta tsige shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun harbi Lieutenant Commodore Awolor da kuma Flight Lieutenant Commodore Okoronkwo, yayin da kuma aka nemi Manjo Kanal Datong aka rasa.

‘Yan bindigar wadanda suka yi shiga irinta sojoji sun wuce masu gadin kofar suka shiga yankin da jami’an suke a cikin makarantar.

Rahotanni dake ta yawo sun nuna cewa daya daga cikin sojojin da ya ji ciwo yana karbar magani a cikin asibitin makarantar ta sojoji.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Rubuta Sharhi