20.1 C
Abuja
Friday, December 9, 2022

Ga ‘yan mata masu sha’awar shiga fim, kada su shigo, inji Saratu Zazzau, Dr Grema a Kwana Casa’in

LabaraiKannywoodGa 'yan mata masu sha'awar shiga fim, kada su shigo, inji Saratu Zazzau, Dr Grema a Kwana Casa'in

Saratu Zazzau, wacce ta bayyana a cikin shirin fim mai dogon zango na Kwana Casa’in ta ba mata masu shirin shiga fim shawarwari, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

A wata hira da Aminiya Daily Trust ta yi da ita, ta shawarci masu shirin fara fim akan kada su shiga, idan kuma ya zama dole to su samu jagora na gari wanda iyayensu zasu damka su a hannun shi.

saratu zazzau
Ga ‘yan mata masu sha’awar shiga fim, kada su shigo, inji Saratu Zazzau, Dr Grema a Kwana Casa’in

Ta sha tarin tambayoyi akan masana’antar Kannywood har ake cewa matan masana’antar basa zaman aure inda tace sakin aure ya zama ruwan dare a ko ina, kawai na Kannywood ne ya fito fili.

Kamar yadda tace, babu matar da take fatan a sake ta, musamman su ‘yan fim da ke auren masu kudi.

Kamar yadda tace:

“Yan mata masu shirin shiga fim, kada su shigo. Idan kuma tilas sai sun shigo to iyayen su suyi musu rakiya su hada su da wanda zai dinga kula da shige da ficen su da tarbiyyar su a location.”

Ta bayyana yadda bayyanar ta a shirin fim din Kwana Casa’in ya kawo mata nasarori da dama don ta kara shahara kwarai.

Ta ce ita ‘yar siyasa ce, kuma shirin fim din ya taimaka mata kwarai a wannan fannin.

Ta ce ‘yan fim suna zaman aure, kawai kaurin suna ne suka yi. Kuma babu matar da zata so ta yi aure ta fito saboda babu dadi.

Wani bawan Allah ya karbi addinin Musulunci saboda kallon shirin fim din Izzar So da yake yi

A yayin da mutane da dama suke yiwa ‘yan shirin fina-finan Hausa na Kannywood kallon mutane dake bata tarbiyya da kuma lalata al’ada, sai gashi an samu wani mutumi ya karbi addinin Musulunci sakamakon kallon fim da yake yi.

Wani rahoto da muka ci karo dashi a shafin Facebook na Kannywood, ya nuna yadda wani bawan Allah ya canja addini zuwa addinin Musulunci sakamakon kallon fim din Izzar So da yake yi.

Mutumin da aka bayyana sunan shi da John, ya fito tun daga karamar hukumar Idom dake cikin jihar Cross Rivers, domin ya karbi kalmar Shahada, inda daga baya ya canja sunan shi zuwa Umar.

A bidiyon da shafin na Kannywood ta wallafa an nuno mutumin tare da shahararren jarumin nan Lawal Ahmad da kuma wasu mutane a lokacin da ake karanta masa kalmar shahada yake biyawa, inda a kasan bidiyon aka yi rubutu kamar haka:

“Masha Allah A Yaune Mukayi Babban Kamu A Musulunci Inda Wannan Bawan Allah Ya Shiga Musulunci Saboda Kallon IZZAR SO Da Yakeyi, Tun Daga Cross river, idom Ikon Local Government Cross River Yanzu Haka Dai Ya Karbi Musulunci, Kuma Yanzu Haka Sunansa Ya koma Umar Daga John, Munayi Masa Addu a Allah Yasa Ya shigo Addinin musulunci A Sa a Allah Yasa Ya Amfane Shi, Amin.”

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance:

Shirin Izzar so dai shiri ne mai dogon zango da yake tashe a wannan lokaci, wanda jarumi Lawal Ahmad yake shiryawa.

A baya dai dama jarumi Falalu Dorayi ya taba yin wata magana da yake nuni da cewa akwai mutane da dama da suka karbi addnin Musulunci sakamakon kallon fim din Haussa da suke yi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe