29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Auren Rahama Hassan ya mutu, ta dawo harkar Kannywood

LabaraiKannywoodAuren Rahama Hassan ya mutu, ta dawo harkar Kannywood

Wani bidiyo ya fara yawa a shafukan sada zumuntar zamani wanda fitaccen furodusa, Abubakar Bashir Maishadda ya wallafa a shafinsa ya dauki hankulan mutane da dama.

A bidiyon, wanda Tashar Tsakar Gida ta nuna, an ga tsohuwar jarumar tare da sauran jarumai sanye da hula ta kungiyar mawaka da jarumai ta 13 X 13, inda mai shaddan ya rubuta “Rahama Hassan is back” ma’ana “Rahama Hassan ta dawo”.

rahama h
Auren Rahama Hassan ya mutu, ta dawo harkar Kannywood

Wannan bidiyon ne ya kara bayar da tabbacin cewa auren Rahama Hassan ya mutu saboda babu yadda za ayi da aurenta ta dawo fim har su kai ga yin tsayuwae gab da gab da MaiShadda.

Musamman idan mutum ya kalli yadda jarumar ta dakata da yin fina-finai tun kafin ta yi aure har ta kai ga yin aure.

Ko a shafukan sada zumunta ba a fiye jin ta ba sai jefi-jefi.

Bayyanar Rahama Hassan a daidai lokacin da ‘yan fim suke ta aure ya janyo surutai inda wasu suke cewa dama ko sun yi aure ba sa son zama.

Dama tun a bayan an fi bayar da misalin masu zaman aure kamar ita jaruma Rahama Hassan din, Mansura Isah, Maijidda Abdulkadir, Wasila da sauran su.

Duk da dai akwai wasu jaruman da auren su yake mutuwa amma basa dawowa fim wanda hakan yake sa asirin su ya rufu.

Duk da dai ana cewa aure rai gare shi, ana samun mutuwar aure a cikin mutane amma na ‘yan fim ya fi bayyana kasancewar su sanannun mutane ne.

Muna mata fatan Ubangiji ya sa hakan ne mafi alkhairi kuma ya bata miji na gari ta samu ta sake yin wani auren.

Nazir ka keta mutuncin mu, kuma ka keta mutuncin masana’antar mu ta Kannywood – Abubakar Bashir Mai Shadda

A yayin da Daraktoci da Furodusoshi suka yi caa akan jaruma Ladi Cima suna yi mata raddi a maganar ta, wacce ta bayyanawa BBC Hausa cewa ba a taba bata kudin da ya wuce dubu biyar ba a duk shekarun da ta kwashe tana fitowa a cikin fina-finan Kannywood.

Fitaccen Mawakin nan Nazir M Ahmad ya fito ya goyi bayan ta, inda maganar shi tafi karfi kan jarumi Ali Nuhu da Falalu A Dorayi, da suka fito suka ce suna bawa jarumar kudade masu kauri a duk lokacin da suka sanya ta a fim.

Maganar Nazir ba ta yiwa ‘yan Kannywood dadi ba

To sai dai kuma maganar ta Nazir ba a nan ta tsaya ba, domin kuwa ya bayyana cewa shi da kanshi shaida ne akan abubuwan dake faruwa a masana’anatar, inda har ya bayyana cewa wannan dalili na zulunci shine yasa ake samun koma baya a masana’antar.

Haka kuma Nazir Sarkin waka ya bayyana cewa wasu ma sune suke cire kudi a aljihunsu su biya domin a saka su a fim, ko kuma idan mace ce, sai ta bada jikinta an kwanta da ita kafin a saka ta a cikin fim.

To sai dai kuma wannan magana ta Nazir ba ta yiwa da yawa daga cikin jarumai da daraktocin na Kannywood ba, domin kuwa bai jima da sakin wannan bidiyo na shi ba, fitaccen daraktan nan Abubakar Bashir Mai Shadda ya fito yayi masa martani a wani bidiyo.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe