An hana masu sanya kananan kaya da gajerun wando shiga masallacin Ka’aba da Masallacin Annabi SAW

You are currently viewing An hana masu sanya kananan kaya da gajerun wando shiga masallacin Ka’aba da Masallacin Annabi SAW
An hana masu sanya kananan kaya da gajerun wando shiga masallacin Ka'aba da Masallacin Annabi SAW


Masarautar Saudiyya ta bada sanarwa cewa duk wani Alhaji da ya sanya kananan kaya ko gajerun wando, baza’a barshi ya shiga masallacin Ka’aba ba da kuma masallacin Annabi SAW dake Madina.

Duk kuma wanda aka samu ya karya wannan doka to za’a ci tarar sa daga Riyal 200, kimanin Naira dubu ashirin da biyu, 22,000 zuwa Riyal 500 kimanin Naira dubu hamsin da hudu 54,000.

An hana masu sanya kananan kaya da gajerun wando shiga masallacin Ka'aba da Masallacin Annabi SAW
An hana masu sanya kananan kaya da gajerun wando shiga masallacin Ka’aba da Masallacin Annabi SAW

Bayanin dokar yana kunshene a cikin wani jawabi da hukumar hajji da umara ta kasar ta fitar, wadda aka wallafa a cikin mujallar ‘Haramain Syarifain’, ranar Juma’a 18 ga watan Fabarairu. 


A fadar mahukuntan kasar Saudiyyar, sanya kananan kaya a masallatai da kuma hukumomin gwamnati, ya sabawa da sabbin kyawawan dabi’un zamantakewa da aka kaddamar. 


Haka kuma, hukumomin sun ce, sanya kananan kaya ga mata a waje bazai zama laifiba saidai idan a cikin masallaci ne. 


An kaddamar da sabbin tarar ne jim kadan bayan ministan harkokin cikin gida Abdulaziz Bin Saud Bin Naif, ya fitar da dokokin zamantakewa na hukumar. 

A cikin dokar, karan-tsaye ga dokar kyawawan halin zamantakewa guda 19 wanda idan aka yi shi mutum ya cancanci hukunci ta shekarar 2019, yanzu an mayar dasu  sun  koma guda 20. A fadar hukumar, duk wanda yayi karan-tsaye ga ko wacce doka a cikin jerin dokokin za’a iya cin tarar sa daga Riyal hamsin 50, har zuwa Riyal dubu shida 6,000. 

Wasu daga cikin dokokin dama, haramun ne aikata su a kasar Saudiyya, amma babu wani matakin horo da aka dauka a baya sakamakon karya su, alkalai kawai sai dai su fadesu. 


An kaddamar da shirin daukar matakin horo sakamakon karya doka tun a ranar 2 ga watan Nuwambar shekarar 2019. A hukumance ta karu akan dokokin zamantakewar al’umma, inda ta alkawarta cin tara, ko dauri ga duk wanda aka samu da halin rashin da’a da ya kai ga babban laifi ko ga jikkata al’umma. 


Jama’a da dama sun yaba da matakin hukumar Saudiyyar, inda suka bayyana shi a matsayin ” kwakkwaran mataki”
Tsohon shugaban hukumar kula da tarbiyyar jama’a, Badr Al Zayani, yace gajeren wando da yake sama da gwiwa, wannan ma ya sabawa da kyakkyawar shiga ta cikin jama’a. Sannan ya jadda hankalin matasa, da su dinga kula da yanayin shigarsu. 


A ka’idar shari’ah, sanya kaya ga namiji wadanda bazasu rufe masa tun daga saman cibiyarsa har izuwa saman gwiwar sa ba; to bai halatta ba. Haramun ne ga maza su bayyana tsiraicinsu ga kowa in banda matansu. 


Haka kuma, ba’a sanya adduar da aka yi ta, al’aura tana waje, a cikin lissafi.

Za a dinga cin tarar Naira 100,000 ga duk wanda ya kunna waka a lokacin da ake kiran Sallah a Saudiyya

Kasar Saudi Arabia, ta Sanya tarar Riyal dubu daya 1000 SR, ga duk wanda ya kunna kida, yayin da ake kiran sallah. Ana yin kiran sallah ne sau biyar a ko wacce rana a cikin amsa kuwwa. ( laasfika ). 

An gabatar da sabbin tarar ne jim kadan bayan ministan cikin gida Abdulaziz Bin Saud Bin Naif, ya fitar da dokar hukumar, wadda take nuna sauyi ga kyawawan dokokin zamantakewa. 

Tarar Riyal dubu daya 1000 ko 2000

Duk wanda aka kama ya kunna kida yayin da ake yin kiran sallah, to za’a ci tarar sa Riyal dubu daya 1000. Idan kuma ya sake, to tarar zata lunku zuwa dubu biyu 2000.

Dokar za ta hau kan duk wanda ya kure kida yayin kiran sallah ne kadai, da kuma duk wanda ya kure kida a cikin motarsa ta hawa, ko kuma a cikin gidajen mutane. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi