Yadda ‘yan Afganistan ke siyar da kodarsu saboda tsananin yunwa da talauci

  • Post author:
  • Reading time:8 mins read
You are currently viewing Yadda ‘yan Afganistan ke siyar da kodarsu saboda tsananin yunwa da talauci
Yadda 'yan Afganistan ke siyar da kodarsu saboda tsananin yunwa da talauci

Rashin aikin yi, bashi, da rashin abinda zai ciyar da ’ya’yansa a Afganistan, shi ya sa Nooruddin ya yanke shawarar siyar da kodarsa – yawan’ yan kasar Afganistan da ke sayar da kodan su yana karuwa don kawai su ceto iyalan su daga matsin rayuwa.

Wannan dabi’ar abu ne da ya zama ruwan dare kuma gama-gari a yammacin birnin Herat da ke Afganistan har ta kai ga an yi wa wani kauye lakabi da “kauyen masu koda daya”.

Afghanistan
Yadda ‘yan Afganistan ke siyar da kodarsu saboda tsananin yunwa da talauci

“Dole ne ta sani yin hakan saboda ‘ya’yana,” Nooruddin ya shaida wa AFP a cikin gari, kusa da kan iyaka da Iran. Ba ni da wani zaɓi.”

Jama’aar Afganistan suna cikin halin rashi

Afghanistan ta fada cikin halin rashin kudi bayan kwace iko da Taliban ta yi watanni shida da suka gabata. Abin da ke kara tabarbara halin matsi shi ne yaki da aka yi shekaru 20 da suka wuce inda kasar Amurka ta mamaye Afganistan.

Fiye da rabin al’ummar kasar kimanin mutum miliyan 38 ne ke fama da matsananciyar yunwa, kusan kimanin ‘yan Afganistan miliyan 9 ne ke fuskantar barazanar fari, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Taimakon da kasashen ketare ke yi wa kasar abin ya zama tafiyar hawainiya sakamakon takunkumin da Amurka ta kakaba mata.

Tattalin arzikin kasar ya kusa durkushewa bayan da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa suka yanke tallafin kudaden da ake basu tare da daskarar da kadarorin kasar da Amurka ta yi.

Shugaban Amurka Joe Biden a farkon wannan watan ya yanke shawarar hana kimanin dala biliyan 7 a cikin kadarorin Afganistan, tare da mayar da rabin kudaden a matsayin diyya ga wadanda harin satumba 11 ya ritsa da su.

Hukumomi sun yi kira

Hukumomin bayar da agaji da kwararru sun yi kira da a dage takunkumin da aka kakaba wa Taliban, inda suka bayyana cewa matakan na kara ta’azzara matsalar jin kai a kasar.
Wadannan matakan ba karamar illa suka yi wa Afganistan ba mutane kamar Nooruddin, mai kimanin shekaru 32, wanda ya ajiye aikin masana’anta da ya ke yi saboda rage albashinsa da aka yi zuwa 3,000 (kimanin dala $30) jim kadan bayan dawowar ‘yan Taliban, a tunanin sa zai samu aikin da yafi wannan.

Amma, yadda dubban ɗaruruwan marasa aikin yi suka cika ƙasar, samun aiki ya yi wahala.

Rashin makama ya sa shi siyar da kodarsa daya.

“Na yi nadama yanzu,” in ji shi da yake bayyana haka a kofar gidansa, inda yagaggun tufafin su ke rataye a jikin bishiya.
“Ba na iya yin aiki . Ina jin zafi kuma ba na iya ɗaukar abu mai nauyi.”

Iyalinsa a yanzu sun dogara ne ga ɗansa ɗan shekara 12, wanda ke sana’ar goge takalma a kan kudi cent 70 a rana.

Koda ta kai farashin $1,500

Nooruddin na cikin mutane takwas da AFP ta zanta da su da suka sayar da kodarsu domin kawai su ciyar da iyalansu da kuma biyan basussuka – a kan kudin da bai fi dala 1,500.

A Afganistan ana yawan samun masu wannan aika -aika.

“Babu wata doka da ta yi tsarin yadda za a iya ba da gudummawa wajen sayar da sassan jiki, amma izinin mai bayarwa ya zama dole,” in ji Mohammad Wakil Matin, wani tsohon babban likitan tiyata a wani asibiti da ke cikin birnin Mazar-i-Sharif da ke arewacin kasar.

Mohamad Bassir Osmani, likitan fida a daya daga cikin asibitocin da ake yin dashe a Herat, ya tabbatar da “yarda” shine tushen komai.

Kauyen masu koda daya

A wajen garin Herat akwai wani kauye Sayshanba Bazaar, ƙauyen da ya ƙunshi ɗaruruwan mutanen da suka shafe shekaru suna zaune a garin.

Wanda aka fi sani da “kauyen masu koda daya”, mazauna kauyen da dama sun siyar da sassan jikinsu bayan da labarin ya zo musu a kan irin kudaden da ake samu.

A gida daya kawai, mutum biyar sun siyar da kodarsu a cikin shekaru hudu da suka wuce, suna tunanin hakan zai tsamo su daga talauci.

“Har yanzu muna fama da bashi ga kuma talauci kamar yadda muka kasance a da,” in ji Ghulam Nebi, yana nuna tabonsa.


A ƙasashen da suka ci gaba, masu ba da gudummawar sassan jiki da masu karɓa yawanci suna ci gaba da gudanar da rayuwar su kamar da, tare da kula da lafiyar su bayan tiyata sosai – kuma sun dogara da rayuwa mai kyau da abinci mai gina jiki.

Wannan kayan alatu galibi ba ya samuwa ga marasa karfi a Afganistan wadanda ke siyar da kodar su kuma har yanzu suna samun kansu cikin talauci – ga kuma rashin lafiya.

Matin ya ce kalilan daga masu ba da gudummawa ne kawai suke zuwa ganin likita bayan an cire.

“Babu cibiyoyin kiwon lafiya da za su yi rajistar masu siyar da koda da masu ba da gudummawa don yin gwaje-gwaje akai-akai don duba tasirin lafiyarsu,” in ji shi.


Shakila, mahaifiyar yara biyu ‘yar shekara 19, ta yi aikin ne jim kadan kafin ‘yan Taliban sun karbe mulki,
Ba mu da zabi saboda yunwa,” in ji Shakila, wacce ta ke sanye da gyale lullube da fuskarta.

Ta sayar da kodarta akan dala 1,500 – yawancinsu sun yi haka ne don biyan dimbin bashin da ke kansu.

Ita kuma mahaifiyar ‘ya’ya uku Aziza, tana jiran sa’ar ta bayan ta hadu da wani ma’aikacin asibiti da ke kokarin hadata da wanda zata ba kodar ta.


“Ya’yana suna yawo a kan tituna suna bara,” kamar yadda ta shaida wa AFP, hawaye cike da idonta.

“Idan ban sayar da koda ta ba, za a tilasta ni in sayar da ‘yata ‘yar shekara daya.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi