Gwamnatin tarayya ta amince a miƙa Abba Kyari ga Amurka domin fuskantar shari’a

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Gwamnatin tarayya ta amince a miƙa Abba Kyari ga Amurka domin fuskantar shari’a

A ranar Alhamis gwamnatin tarayya ta amince da bukatar da ƙasar Amurka, tayi na a mika mata dakataccen DCP na ‘yan sanda, Abba Kyari, bisa alakarsa da shahrarren dan damfarar yanar gizo Abass Ramon wanda akafi sani Hushpuppi da kuma wasu mutum hudu. Jaridar Vanguard ta rahoto

An shigar da ƙara a gaban kotu

Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN) ya bayyana hakan a karar da ya shigar gaban shugaban Alkalan babban kotun tarayya dake Abuja kan lamarin.

An shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/249/2022 karkashin dokar Extradition Act. Wannan kara da ya shigar ya biyo bayan bukatar Abba Kyari da wakilin jakadan Amurka yayi a Abuja.

Roƙon da akayi a ƙarar shine:
“Domin miƙa Abba Kyari, wanda yake fuskantar tuhumomi guda uku”

Antoni Janar ya bayyana cewa lallai ya gamsu da cewa zargin da ake yiwa Abba Kyari ba tada alaka da siyasa kuma babban laifi ne.

Ya bayyana cewa:

“Idan aka mikashi ga ƙasar Amurka, ba za’ayi masa rashin adalci ba, ba za’a azabtar da shi ba, ba za’a hanashi yancinsa ba saboda launin fatar jikinsa, asalinsa ko siyasarsa ba.”

Ba ayi masa rashin adalci ba

Abubakar Malami ya kara da cewa duba da irin laifukan da ake zargin Abba Kyari da su, ba za’a ce an yi masa rashin adalci ba idan aka mika shi ga ƙasar Amurka ba.

Abubakar Malami ya bayyana cewa ya gamsu cewa an zargi Abba Kyari bisa laifin da ake son a miƙa shi.

Yayi nuni da cewa Abba Kyari bai fuskantar tuhuma a Najeriya makamanciyar wacce ake masa a ƙasar Amurka.

Zargin safarar hodar Iblis: Yadda Abba Kyari ya yi aiki da ƙungiyar ƙwaya a Brazil – NDLEA

Hukumar ‘yan sanda ta ba da sanarwar damƙe Abba Kyari a ranar litinin da ta gabata ne dai bayan kiran da aka yi na nemansa ido rufe game da safarar miyagun kwayoyi kamara yadda NDLEA ke zarginsa.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA, ta nesanta jami’anta daga cinikin hodar ibilis mai nauyin kilogiram 25 da suka haɗa kai da gungun ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari.

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya yi zargin cewa jami’an hukumar a filin jirgin Enugu ne suka samu labarin alfadarin da ya kawo haramtattun abubuwa daga birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi