Ƙungiyar matasan arewa ta caccaki Dangote kan ƙarin farashin kuɗin siminti

  • Post author:
  • Reading time:4 mins read
You are currently viewing Ƙungiyar matasan arewa ta caccaki Dangote kan ƙarin farashin kuɗin siminti

Ƙungiyar matasan arewa watau Northern Youths Council of Nigeria of Nigeria (NYCN) tayi Allah wadai da bayyana cin gagarumar ribar naira biliyan N500 kafin cire haraji da ribar naira biliyan N350 bayan cire haraji da kamfanin simintin Dangote yayi, inda ta jajirce kan cewa kuɗin da aka bayyana alamu ne da ke nuna yadda ‘yan Najeriya ke shan kashi a hannun wasu tsiraru waɗanda gwamnati ke taimakawa ta hanyar  ba su kariya.

Ana sayar da siminti fiye da farashin sa

A wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba wacce shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamyared Isah Abubakar, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta bayyana cewa kuɗin buhun siminti mai nauyi kilogram 50 ya ƙaru a kasuwanni, inda yanzu haka ake sayar da shi a fiye da kaso 240 na ƙarancin farashin sa a duniya, duk kuwa da cewa talauci yayi wa ‘yan Najeriya katutu. Jaridar Independent.ng ta rahoto

Dangote ya sha suka

Sanarwar na cewa:

Yankin arewacin Najeriya inda Aliko Dangote ya fito shine yake da kaso mafi rinjaye na talauci da kuma wasu abubuwan ban tsoro na rashin tattalin arziƙi da makamantan su.

“A maimakon ya sauƙaƙawa ‘yan Najeriya, Alhaji Aliko Dangote yana can yana tabbatar da cewa talakawan Najeriya sun zama matsiyata a ƙasar su ta hanyar ƙara tsawwala kuɗaɗen abubuwan masarufin da yake da iko a kai.

Ƙungiyar ta faɗa a cikin sanarwar

Farashin sikarin Dangote ya faɗi da sama da N11b a kasuwa yayin da rikicinsa da BUA ke tsananta

Yaƙi tsakanin sigan Dangote da kayan abincin BUA ya koma kasan kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya inda sigan Dangote ta sha kashi.

Yayin zaman ciniki a ranar Laraba, Fabrairu 23, 2022, Kamfanin Dangote Sugar Refinery Plc ya faɗi da kashi 5.28 cikin 100.
Babban kasuwar kamfanin ta ragu daga Naira biliyan 218 zuwa Naira 207.10 inda ya rufe kan Naira 17.05 kan kowane kashi PAY.

Yaƙin wanda ya zama babban ɗan wasa mafi girma a masana’antar sukari da alama yana tafiya hanyar BUA Foods wanda ya zargi Dangote Sugar kwanan nan da son haifar da ƙarancin sukari na wucin gadi.

A ranar Laraba, 23 ga Fabrairu, 2022 ciniki, farashin hannun jarin kamfanin Dangote Sugar Refinery Plc ya sauka da kashi 5.28 cikin 100, inda ya rufe kan Naira 17.05 kan kowacce kaso, inda farashin kasuwar ya tashi daga Naira biliyan 218 zuwa Naira biliyan 207.10.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

This Post Has 2 Comments

  1. nafi'u Abdullahi

    One bag of cement is 4200 in my area

  2. Muhammad Usman Matawalle

    Allah muna rokonka duk Wani Mai sa hannu wajen azabtar damu dakuma wahalar damu cimana Amana da cutar damu
    Allah ka Saka mana

Rubuta Sharhi