Masu kare hakkin shanu sun kashe wani musulmi a kan zargin fasa-kwabrin shanu a Indiya

You are currently viewing Masu kare hakkin shanu sun kashe wani musulmi a kan zargin fasa-kwabrin shanu a Indiya
Masu kare hakkin shanu sun kashe wani musulmi a kan zargin fasa-kwabrin shanu a Indiya

‘Yan kwanakin na kafar yanar gizo ta karade da bidiyon wani musulmi da aka gan shi wasu wadanda suka ce su masu kare hakkin shanu ne suna dukansa har ya mutu, a garin Bihar. 
A rahoton kananan kafofi, sun ce an kashe shi kuma aka yi kokarin kona gawarsa, bayan sun yaryada mata fetur. A wani hoton kuma cewa aka yi, sun yaryada masa gishiri ne a jikin sa kafin su binne shi. 

Shunu
Masu kare hakkin shanu sun kashe wani musulmi a kan zargin fasa-kwabrin shanu a Indiya


Mamacin wanda aka bayyana a matsayin Mohamad Khaleel Alam, dan jam’iyyar Janata Dal ne daga gundumar Samastipur.

Yadda mamacin ya dinga rokon masu kare shanun su kyake shi

An gan shi a cikin bidiyon ya durkusa yana neman afuwa a gaban wani wanda ya nade hannu yana tsaye, inda yake rokon su da su saka shi ya tafi.

Makashin wanda ya rufe fuskarsa da kyalle a bidiyon, cikin rashin imani, ya tambayi mamacin da ya bayyana inda aka yanka shanun, sannan kuma ya fadi sunayen wadanda suke siyar da shanun. 

Haka kuma, sun tambaye shi sau nawa ya ci naman shanu a rayuwar sa, da kuma wanda ya baiwa ‘ya’yan sa suka ci. Sun kara da tambayar sa cewa ko Qur’ani ya bada damar cin naman shanu?  Inda rikitaccen mamacin ya ce a’a. 

Bidiyon wanda ya cika da kalaman nuna kiyayya, ya zagaya tare da wadansu cin zarafi da ake yi wa musulmai. Amma abin takaici, wani kurtun ‘dan sanda ya musanta zargin, inda yace kawai ana son karkatar da hankalin jama’a ne domin a danne batun kisan. 
A sakon sa na Twitter, shugaban adawa na Bihar Tejashwi Yadav, ya jaddada rashin jin dadin sa a kan lamarin. Da yake magana a sakon Twitter din da harshen Indiyanci, yace babban minista Nitish Kumar ne yake da alhakin bayani a kan abin da yake faruwa a Bihar. 
A ranar Juma’a, 19 ga watan Fabarairu, an tsinci gawar Khaleel din a bakin gabar kogin Burhi Kadak, inda aka birne shi a cikin yashi. 
Tun da farko, dangin mamacin sun shigar da rahoton batan ‘dan uwan nasu tun a ranar 16 ga watan Fabarairu. Amma sai da suka dinga samun kira daga wayar mamacin, inda ake tambayar su kudi.

Mai kiran yana cewa ne ya ranci lakh biyar 5 ne kuma yana barazanar siyar da kodar mamacin, idan dangin nasa basu bayar da kudin ba. 

Yadda wani bidiyo ya nuna ‘yan sanda a Indiya na dukan mata Musulmai da suka fito yin zanga-zangar hana su sanya Hijabi

Yayin wata zanga-zangar adawa ta dokar hana sa hijabi a Uttar Pradesh ta Ghaziabad da ke kasar Indiya an ga ‘yan sandan jihar sun farwa mata Musulmai da ke sanye da hijab da duka.

Yayin da zanga-zangar ke cigaba da gudana a wasu da ga cikin jihohin kasar a bisa kan dokar hana sa hijabi a kwalejoji, hatsaniyar ta fara ne a Karnataka wanda har ta kai ga an shiga kotu.

Rundunar ‘yan sandan ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike kan faifan bidiyon da ya yadu a shafukan sada zumunta inda wasu suke suka tare da caccakan ‘yan sandan.

Yan sanda sun gabatar da rahoto ga me da lamarin

Dangane da lamarin da ya faru a ranar Lahadin da ta gabata, ‘yan sanda sun gabatar da rahoton farko game da bayanan abun da ya faru.

A rahoton da ‘yan sandan suka fitar, rundunar ‘yan sandan ta ce ta samu labarin cewa wasu matan Musulmi kimanin su 15 dauke da takardu na nuna adawa da gwamnati sun taru a hanyar Sani Bazaar a Ghaziabad ba tare da an basu izini ba. FIR ta ruwaito cewa matan sun fara rera waka ne a lokacin da tawagar ‘yan sanda ta iso wurin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]m

Rubuta Sharhi