Manyan Kasashen duniya 10 da suka fi sauran kasashe arzikin man fetur a shekarar 2022

  • Post author:
  • Reading time:7 mins read
You are currently viewing Manyan Kasashen duniya 10 da suka fi sauran kasashe arzikin man fetur a shekarar 2022
Manyan Kasashen duniya 10 da suka fi sauran kasashe arzikin man fetur a shekarar 2022

Idan aka ga wani batu da ya shafi arzikin man fetur na kasashe daban-daban, hankali yana karkata kan kasar Saudiyya domin an san cewa za ta kasance kan gaba, amma abin mamaki ba haka zancen ya ke ba.


Ga jerin jaddawalin kasashe 10 da ke da arzikin mai, wanda kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta fitar. Jimillar arzikin mai a duniya an kiyasta ya kai ganga tiriliyan 1.48.

Man fetur
Manyan Kasashen duniya 10 da suka fi sauran kasashe arzikin man fetur a shekarar 2022
  1. Venezuela kasar tana samar da mai kimanin biliyan 304,sannan a kowace rana tana fitar da mai ganga 2,489


2. Saudiyya-kasar saudiyya tana samar da mai kimanin biliyan 259,sannan a ko wacce rana tana fitar da ganga 11,545.7 na mai.
3. Iran-kasar iran tana samar da mai kimanin biliyan 209 wanda a kowacce rana tana fitar da ganga 3,538 na mai.

4. Iraqi – kasar Iraqi tana samar da mai biliyan 145 sannan a kowacce rana tana fitar da ganga 2,986.6 na mai

5. Kuwait – kasar Juwait tana fitar da mai kimanin biliyan 102,sannan a kowacce rana tana fitar da ganga 2,796.8 na mai.

6. Daular Larabawa – Daular larabawa tana iya samar da mai kimanin biliyan 98 sanan tana fitar da ganga 3,213.2 na mai a kowacce rana.


7. Rasha – kasar Rasha tana samar da mai kimanin biliyan 80,wanda a kowacce rana tana iya fitar da mai kimanin ganga 10,397a kowacce rana.

8. Libiya – kasar Libiya ta na samar da mai biliyan 48,sannan a kowace rana tana fitar da mai ganga 1,483.

9. Najeriya – Najeriya tana da mai kimanin biliyan 37 sannan a kowacce rana tana fitar da mai ganga 2,524.1

10. Amurka -kasar Amurka bata kasance kasa mai arzikin mai ba amma ta kasance kasar da take iya sarrafa mai wanda ya kai kimanin ganga Biliyan 47

Kasashe masu arzikin man fetur za su rage man da suke fitarwa

Bangarorin sun amince a zabge ganga miliyan 9 da dubu 700 da suke samarwa kullum, bayan shafe tsawon mako guda suna tattaunawa.

Da farko kasashen sun kuduri aniyar rage ganga miliyan goma ne a kullum, wanda ya kai kimanin kashi 10 cikin 100 na man da ake fitarwa kasuwannin duniya, sai dai Mexico ta sa kafa ta shure adadin da aka nemi ta rage.

Kasashen masu arzikin man fetur za su fara rage man da suke hakowa ne daga ranar 1 ga watan gobe, kuma yarjejeniyar za ta kai har karshen watan Yuni, daga nan kuma za a fara sassauta matakin sannu a hankali har zuwa shekara ta 2022.
Tun a farkon watan jiya ne farashin man fetur ya yi faduwar da bai taba yin irin ta ba kusan a cikin shekara ashirin.

Haka zalika, bukatun man fetur din sun yi matukar raguwa sakamakon annobar corona, abin da ya kara ta’azzara lamarin.

Wani kwararre kan harkar makamashi, Sandy Fielden, ya fada wa BBC cewa yarjejeniyar ba a taba ganin irinta ba saboda ba kawai a tsakanin kungiyar OPEC ba ne da Rasha har ma da kasar da ta fi samar da man fetur a duniya wata Amurka da kuma sauran kasashen kungiyar G-20.

Ya ce yarjejeniyar tana da matukar muhimmanci don kuwa: “Komai ya dogara ne a kan makamashi.
A yanzu, tabbas babbar matsalar da ta fi damun harkokin man fetur ita ce ba ma amfani da makamashi mai yawa saboda an rufe kasashe ba shiga ba fita.

“Man fetur da ababen sufuri ke sha ya yi matukar raguwa da kimanin kashi daya cikin uku.”

Shugaba Donald Trump dai ya bayyana lamarin a matsayin wata gagarumar yarjejeniya. A ‘yan kwanakin nan ya yi ta matsa wa Mexico lamba, wadda ta ki amincewa ta rage nata.

Rikicin sanya hijabi a kasar Indiya ya sanya wata kwalejin gwamnati ta kori dalibai musulmai 58

A garin Shiralakoppa da ke kudancin Karnataka, dalibai 58 ne suka gudanar da zanga-zangar adawa ga hukumar kwalejin bayan da aka dakatar da su saboda sun ki cire lullubin su.

Daliban sun fito ne daga Kwalejin Gwamnati da ke Shiralakoppa. Bugu da kari, an kuma samun karin tashe-tashen hankula a gundumomin Belagavi, Yadgir, Bellary, Chitradurgam, da Shiamogga, inda dalibai sanye da hijabi da Niqab suka yi kokarin kutsa kansu cikin ajujuwa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi