Muhimman amfani 8 na aure ga mata da maza da kuruciyarsu

You are currently viewing Muhimman amfani 8 na aure ga mata da maza da kuruciyarsu
https://www.labarunhausa.com/9004/kishi-yasa-wata-matar-aure-ta-kashe-mijin-ta-har-lahira-a-jihar-nasarawa/

Mafi yawan mutane su kan ce ba za su yi aure ba sai sun tanadi komai, kamar gida, mota aiki mai kyau. Amma mai yiwuwa akwai bukatar sake tunani a kan. A Wannan rubutu zamu tattauna dalilai guda takwas 8 wadanda domin su mutum ya kamata yayi aure da wuri.

Auren wuri
Muhimman amfani 8 na aure ga mata da maza da kuruciyarsu
  1. Fahimtar juna

Yin aure da wuri yana baiwa maaurata dama su fahimci junan su. Yin hakan zai sa kowa ya san abinda kowa ke so da wanda baya so domin farantawa juna da kuma gudun sabawa juna.

  1. Tafiyar ku duk inda kuke so

Na biyun kuwa, abu ne da yake bijirowa kai tsaye. Idan mutum yayi aure da kuruciyar sa, hakan zai bashi damar ya tafi duk inda yake so da budurwar sa ahhh ! Ina nufin matarsa, babu wanda zai sanya musu ido.

  1. Saduwar aure

Yin aure da wuri yana bai wa mutum damar more saduwar aure. Saduwar aure abu ne da namiji da mace suke bukata a koda yaushe. karsashin ta yana kara raguwa idan mutum ya manyanta.

Yin aure da wuri zai sanya ka cashe wannan rayuwa cikin nishadi, ba kamar idan ka manyanta kayi aure ba. Fatan kun gane.

  1. Kar ka ware lokacin aure

Wasu mutanen su kan ce ai su lokacin su bai yi ba, ko ba su shirya ba, sai su ki yin aure koda kuwa sun sami budurwar da za su aura.

Ni kuwa sai nake ganin, da yin aure kana shekara 20, da yinsa kana shekara 40 duk aure ne, malam kawai idan kana da hali kawai ka yi aure kana 20 tunda komin daren dadewa sai kayi shi.

  1. Zama aboki ko kawar `yayan ku

Wasu mutanen na ganin haifar ‘yaya da wuri, zai rage musu wani jin dadi, sun manta da baiwar dake cikin samun ‘ya’ya kana dan shekara 28.

Zaka iya zama abokin su, ku je ko ina ba tare da kana da wata tawaya ba, ka basu kyakkyawar tarayya da kwarin ka.

  1. Za ka sami kima da mutuncin

Yin aure da wuri ya na baiwa mutum kima da darajar, yana mayar da mutum babba alhalin shi yaro ne, ta yadda za a dinga shawara da shi, zai dauki wasu nauyuka da kuma kike gurabe da dama a cikin dangin mutum.

  1. Hana mutum aukawa cikin aikata Zina

Na biyun karshe, abu mai mahimmanci ga kuruciya shi ne, Idan mutum ya kai shekara 20 karsashin sha’awar sa zai karu sosai ta yadda wani zai iya karkata zuwa fadawa neman yadda zai gamsar da bukatar sa ta jima’i.

Idan ka na da aure, duk ba za ka yi wannan gurbataccen tunanin ba.

  1. Sake yin Aure

Mai yiwuwa, ba za ku so wannan ba, amma tilas idan aka zauna dole a saba. Wani sabanin yana iya janyo wa a rabu.

Idan an sami akasin rabuwa ba fata ake yi hakan ya faru ba, to mutum yana da damar da zai kara yin wani auren saboda yana da jini a jika.

Kishi yasa wata matar aure ta kashe mijin ta har lahira a jihar Nasarawa

Wata matar aure mai suna Atika ta daɓa wa mijinta wuƙa har lahira a garin Mararraba dake ƙaramar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

Lamarin dai kamar yadda City & Crime suka gano, ya faru ne a daren ranar Asabar.

Ibrahim Salihu mai shekaru 37, makanike, an ce ya je dakin Atika, wacce ita ce matarsa ​​ta farko, domin yi mata bankwana, ya tafi dakin matar sa ta biyu da suke gida ɗaya.

City & Crime sun tattaro cewa Salihu ya kasance yana kwana biyu tare da kowacce daga cikin matan a kan jujjuyawa kuma yana da dabi’ar bankwana da kowa a duk lokacin da zai tafi ɗakin ɗayar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi