Wani Likita a kasar Saudiyya ya gana da wasu tagwaye da ya raba shekaru 13 da suka gabata

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
You are currently viewing Wani Likita a kasar Saudiyya ya gana da wasu tagwaye da ya raba shekaru 13 da suka gabata
Wani Likita a kasar Saudiyya ya gana da wasu tagwaye da ya raba shekaru 13 da suka gabata

‘Yan biyun lokacin da aka haife su an haife su ne a manne da juna a kasar Saudiyya. Yawancin gabobin jikinsu kamar su hanji da mafitsara suna hade ne wuri daya.
Abdallah Al-Rabiah, babban mai kula da Cibiyar Bayar da Agajin Gaggawa ta Sarki Salman (KSrelief), ya gana da Hassan da Mahmoud a ranar Laraba wadanda a da sassan jikin su yake a hade. ‘Yan asalin kasar Masar ne, amma mazauna birnin Riyadh, kimanin shekaru 13 kenan bayan da aka yi nasarar raba su a wani aikin tiyata da aka yi musu a garin Riyadh.

Conjoined
Wani Likita a kasar Saudiyya ya gana da wasu tagwaye da ya raba shekaru 13 da suka gabata

Likitoci a asibitin King Abdulaziz Medical City sun yi wa tagwayen tiyata a shekarar 2009 a lokacin da suke da watanni 9 kacal. An hade su a cikin ciki kuma an raba wasu gabobin jiki da sassan jiki, ciki har da hanji da kuma fitsari.

Al-Rabiah ya ce masarautar za ta ci gaba da zama fitila ga mabukata da marasa galihu a duk fadin duniya. Shirin likitancin da aka raba Hassan da Mahmoud, wani karin girma ne na ayyukan jin kai na kasar, in ji wanda ake gudanarwa a karkashin umarnin Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman na kasar Saudiyya.

Tagwayen dai sun samu rakiyar iyayensu ne a ziyarar da suka kai babban birnin kasar Saudiyya, inda suka gode wa jama’a da gwamnatin kasar Saudiyya bisa shirya yi wa ‘ya’yansu tiyata. Lafiyar yaran ya inganta a tsawon shekaru, in ji su.

Za a dinga cin tarar Naira 100,000 ga duk wanda ya kunna waka a lokacin da ake kiran Sallah a Saudiyya

Kasar Saudi Arabia, ta Sanya tarar Riyal dubu daya 1000 SR, ga duk wanda ya kunna kida, yayin da ake kiran sallah. Ana yin kiran sallah ne sau biyar a ko wacce rana a cikin amsa kuwwa. ( laasfika ). 

An gabatar da sabbin tarar ne jim kadan bayan ministan cikin gida Abdulaziz Bin Saud Bin Naif, ya fitar da dokar hukumar, wadda take nuna sauyi ga kyawawan dokokin zamantakewa. 

Tarar Riyal dubu daya 1000 ko 2000

Duk wanda aka kama ya kunna kida yayin da ake yin kiran sallah, to za’a ci tarar sa Riyal dubu daya 1000. Idan kuma ya sake, to tarar zata lunku zuwa dubu biyu 2000.

Dokar za ta hau kan duk wanda ya kure kida yayin kiran sallah ne kadai, da kuma duk wanda ya kure kida a cikin motarsa ta hawa, ko kuma a cikin gidajen mutane. 

Haka kuma, dokar bata hau kan wanda yake sauraren kida a cikin iyafis ba. 

Tarar Ryal dari biyar 500 idan makoci ya kai karar ka

Bugu da kari kuma, kasar Saudiyya ta sanya karin tara akan duk wanda ya kure kida a cikin gidan sa ya takurawa makwafta, idan har makwaftan suka kai korafi, to zai biya tarar Ryal dari biyar 500. 

Mutane suna kunna kida a waya a Ka’abah

A fadar gwamnatin kasar, ana ganin mahajjata na cikin kasar, ko wadanda suka zo daga wasu kasashen, suna amfani da wayoyinsu na hannu a lokacin da ake yin kiran sallah, wanda yin hakan ya saba da da’a kuma haramunne. 

Saboda haka, mahukuntan kasar Saudi Arabia suke gargadin jama’a da su kiyayi kure  kida a gidajensu, yayin kiran sallah, yayin Iqama da kuma cikin motar hawa. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi