Wani mutum ya halaka wanda ya doke masa karen sa a jihar Gombe, ya shiga hannun ‘yan sanda

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Wani mutum ya halaka wanda ya doke masa karen sa a jihar Gombe, ya shiga hannun ‘yan sanda
'Yan sanda sun kama magidanci da ya kashe kaninsa bayan ya kama shi yana lalata da matar sa

Hukumar ‘yan sandan jihar Gombe, ta tabbatar da cafke Ibrahim Saidu, mai shekaru 25 bisa laifin caka wa wani mai babur, Saley Babayo, wuƙa har ya mutu saboda ya doke masa karen sa da babur.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ishola Babaita, yayin ganawa da ‘yan jarida a Gombe ya bayyana cewa jami’an hukumar na gundumar Akko ne su ka cafke Saidu inda lamarin ya auku. Jaridar Daily Trust ta rahoto

'Yan sanda
Wani mutum ya halaka wanda ya doke masa karen sa a jihar Gombe.

Wanda ake zargin ya fusata

Saidu ya fusata inda ya cakawa Saleh Babayo wuƙa, hakan ya sanya ya mutu, kawai a bisa dalilin ya doke masa karen shi da babur ɗin sa.

Kwamishinan yayi bayanin cewa an garzaya da Babayo zuwa babban asibitin Kumo inda likita ya tabbatar da mutuwar sa.

Ya kuma ƙara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifin sa, sannan za’a miƙa shi gaban kuliya nan ba da daɗewa ba.

News Agency of Nigeria (NAN) ta ruwaito cewa karen bai mutu ba bayan bugun da akai masa, sannan an taso ƙeyar sa da wanda ake zargin zuwa ofishin ‘yan sandan.  

Hukumar ta cafke wasu ɓata gari a jihar

Haka kuma, Babaita ya bayyana cewa an cafke wasu mutum biyar bisa aikata laifin garkuwa da mutane, yayin da kuma aka cafke wasu mutum biyu bisa aikata laifin fyaɗe

An samu bindiga ƙirar AK 47 guda ɗaya da harsashi guda uku a cikin ta sannan kuma an samu adduna guda uku duk a hannun waɗanda ake zargin.

Kwamishinan yayi babban kira ga al’ummar jihar

Ya tabbatar wa da al’umma cewa hukumar a shirye ta ke wajen kawo ƙarshen laifuka da ɓata gari inda ya buƙaci jama’a da su dinga bayar da muhimman bayanai ga ‘yan sanda domin kawo ƙarshen miyagun laifuka.

Sannan kuma Babaita, ya ja kunnen duk wasu masu aikata miyagun laifuka da su shiga taitayin su, inda ya tabbatar da cewa hukumar ba zatayi ƙasa a guiwa ba wajen kawo ƙarshen miyagun laifuka a jihar.

Mata mai ciki ta gurfana a kotu kan garkuwa da kanta, ta siya gida da kudin fansar da ta karba daga masoyinta

Wata mata mai juna biyu mai suna Jamila Ardo, ta gurfana a gaban kotu bisa zarginta da yin garkuwa da kanta tare da karɓar kuɗin fansa a hannun masoyinta.

Matar mai suna Jamila Ardo wacce ta fito daga Wauru Jabbe a karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa, ta yi garkuwa da kanta tare da karɓar kuɗi Naira miliyan biyu daga Mallam Adamu Ahmed da ke babban birnin tarayya Abuja.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi