Rikicin sanya hijabi a kasar Indiya ya sanya wata kwalejin gwamnati ta kori dalibai musulmai 58

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
You are currently viewing Rikicin sanya hijabi a kasar Indiya ya sanya wata kwalejin gwamnati ta kori dalibai musulmai 58
Rikicin sanya hijabi a kasar Indiya ya sanya wata kwalejin gwamnati ta kori dalibai musulmai 58

Rikicin Hijab – A garin Shiralakoppa da ke kudancin Karnataka, dalibai 58 ne suka gudanar da zanga-zangar adawa ga hukumar kwalejin bayan da aka dakatar da su saboda sun ki cire lullubin su.

Daliban sun fito ne daga Kwalejin Gwamnati da ke Shiralakoppa. Bugu da kari, an kuma samun karin tashe-tashen hankula a gundumomin Belagavi, Yadgir, Bellary, Chitradurgam, da Shiamogga, inda dalibai sanye da hijabi da Niqab suka yi kokarin kutsa kansu cikin ajujuwa.

Karnataka
Rikicin sanya hijabi a kasar Indiya ya sanya wata kwaleji gwamnati ta kori dalibai musulmai 58

Rikicin sanya hijabi

Idan ba a manta ba jaridar labarun Hausa ta kawo rahoto makamancin haka inda Wata ɗaliba musulma mai suna Muskan Khan, wacce ta fuskanci tsangwama a wurin masu tsaurin ra’ayin addinin Hindu a kan hanyarta ta zuwa makaranta sanye da hijabi a jihar Karnataka da ke ƙasar Indiya, ta bayyana cewa suna rera mata waka “Jai Shri Ram” saboda ta sanya hijab.

Ita dalibar sai ta ce Allahu Akbar. ‘Zan cigaba da fafutukar neman ‘yancin sanya hijab’.

Daliba sanye da hijabi

An samu hatsaniya sosai a jihar Karnataka ranar Talata bayan an wallafa wani bidiyo a shafin Twitter na wata ɗaliba musulma sanye da hijab ta sha tsangwama a wurin masu tsaurin ra’ayin addinin Hindu.
A cigaba da zanga zangar, an sake samun labari inda aka hangi ‘yan sandan Indiya a wani faifan bidiyo suna dukan matan musulmai da suka fito kan titi suna zanga zanga.

Su kuma a nasu bangaren ‘yan sandan kasar sun fitar da rahoton cewa masu zanga-zangar sun fito kan titi ne ba tare da izini ba.

Rundunar ‘yan sandan ta ce ta samu labarin cewa wasu matan Musulmi kimanin su 15 dauke da takardu na nuna adawa da gwamnati sun taru a hanyar Sani Bazaar a Ghaziabad ba tare da an basu izini ba. FIR ta ruwaito cewa matan sun fara rera waka ne a lokacin da tawagar ‘yan sanda ta iso wurin.

Wasu daga cikin masu zanga zangar sun far wa ‘yan sanda

Wasu maza da suka fito daga cikin tawagar masu zanga-zangar sun fito inda suka fara cin zarafi suna zagin jami’an ‘yan sandan da ke kokarin kora masu zanga-zangar su koma gida, a cewar FIR.

A cewar korafin da ‘yan sandan suka fitar, an bayyana wani mai suna Raees a matsayin daya daga cikin wadanda ake tuhuma , kuma masu zanga-zangar sun yi barazana ga ‘yan sandan.

Gwamnan Kwara ya ce yana goyon bayan amfani da hijabi ga mata musulmai a jihar

Gwamna Abdulrazaq ya ce bayyana matsayar sa game da lamarin ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke a jihar Kwara “gamayyar al’umma wanda bambancinta da zaman lafiyan ta a matsayinta na yankin kudu maso arewa shi ne wuraren siyar ta na musamman.”
Abdulrazaq ya ce gwamnatinsa tana bin doka da kuma gaskiya da adalci a kowanne lokaci.
Hakan ya biyo bayan zargin da al’ummar musulmai da kuma kiristoci a jihar suka yi masa a kan cewa ya ki ya saka baki saboda siyasa.

Iyayen dalibi sun ki karban diyya daga gwamnati

Dangi da ‘yan uwa Musulmai sun ki karban diyyar N1m da gwamnatin gwamna Abdulrazak ta bai wa iyalan Habeeb Idris, yaron da aka kashe a wata zanga-zanga da aka yi kwanan nan a makarantar Oyun Baptist High School dake Ijagbo kan rikicin saka hijabi.
Haka kuma, sauran mutum 11 da suka samu raunuka a rikicin sun yi watsi da Naira 250,000 da gwamnatin ta bayar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

This Post Has One Comment

  1. Suleiman garba

    ya Allah ka la’anci duk Wanda ke da hannu kan kin addinin musulinci da Al Ummar musulmai, ya hayyu ya kayyum.

Rubuta Sharhi