Wani Mahaifi ya kashe diyarsa mai shekara 5 har lahira da duka saboda ta kasa yin aikinta na makaranta 

You are currently viewing Wani Mahaifi ya kashe diyarsa mai shekara 5 har lahira da duka saboda ta kasa yin aikinta na makaranta 
Wani Mahaifi ya kashe diyar sa har lahira da duka saboda ta kasa yin aikinta na makaranta 

Mahaifin wata matumburar yarinya, ya fusata sakamakon kasa yin aikinta na makaranta da ya koya mata saboda bata gane koyarwar da yayi mata. 

Mahaifin dan asalin gasar Egypt, ya rufe diyar tasa da duka da dankon roba, inda ya lakada mata duk a jikin ta har yayi rudu-rudu. Ta yi ta kuka tana neman agaji amma mahaifin nata bai daina dukanta ba. 
Yayi mata mummunan rauni a kanta da kirjinta, ta yadda ba za ta iya jure radadin ciwon ba, inda tace ga garin ku nan. 

mahaifi
Wani Mahaifi ya kashe diyar sa har lahira da duka saboda ta kasa yin aikinta na makaranta 

“Zan dinga yin aikin gida da kaina baba, ka yi mini afuwa kar ka kasheni, nice fa diyarka baba “-

Tana kara lokacin da mahaifin yana dukanta da dankon roba. Karar da take yi ita ce ta janyo hankalin makwabta. 

Koda makwabta suka zo, sai suka iske har mahaifin ya hallaka yarinyar, wacce aka kashe kawai domin ta kasa yin aikin gidan da aka basu a makaranta, wanda kuma hakan ya faru ne saboda ta kasa gane koyarwar mahaifin ta. 


‘Yan sandan Cairo sun cafke mahaifin, wanda ya bayyana cewa ba ya doketa domin ya kashe ta ba ne.

Yadda makwabci na ya kashe ‘ya ta mai shekara 8 bayan na biya kudin fansa N3m – Magidanci daga Zaria

Wani mutumin Zaria, Alhaji Shu’aibu Wa’alamu, ya bayyana yadda aka yi garkuwa da ‘yar sa ‘yar shekara 8 tare da kashe ta bayan ya biya masu garkuwa da mutanen kudin fansa Naira miliyan uku.

Da yake magana a wata hira da jaridar Vanguard, Shuaibu Wa’alamu ya ce an sace ‘yar sa, Asmau, a ranar 9 ga watan Disamba 2021, kuma da ta kasa komawa gida, ya kai kara ga ‘yan sanda.

Bayan wasu kwanaki, masu garkuwan sun fara kiran lamba ta suna neman N15m. Amma mun tattauna kuma na fara ba su N2m. Sun karbi kudin ne a unguwar Rigasa da ke Kaduna. Daga baya, sai suka sake kira na suka bukaci a ba wdaani N1.045m a matsayin kawai sharadin sakin ‘ya ta.

‘’Ban yi gardama ba na ba su kuɗin. Sai dai bayan sun biya kudin fansa kamar yadda aka nema a ranar 19 ga watan Janairu, sai suka kira ni suka ce min sun kashe ta ne kuma suka kashe wayar. Kun ga tun farko ina bin wadanda suka sace ta muna yin abin da suka ce saboda tsoron rasa ta, yanzu sun kashe ta .

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Rubuta Sharhi