Mai rubutun adon Kiswa na Ka’aba Rajab Mahoos ya rasu bayan hidima ta shekara 47

You are currently viewing Mai rubutun adon Kiswa na Ka’aba Rajab Mahoos ya rasu bayan hidima ta shekara 47
Mai rubutun adon Kiswa na Ka'aba Rajab Mahoos  ya rasu bayan hidima ta shekara 47


Dan asalin kasar Saudi Arabia mai suna Rajab Mahoos Al maliki, daya daga cikin manyan masu yin kwalliyar zinare na dakin ka’aba, ya rasu bayan ya shafe shekara 47 yana hidimar dakin Ka’aba. 


A Saudi Arabia akwai wani birnin na musamman da aka ware domin yin ado ga dakin ka’aba  wanda aka fi sani da Kiswa. 

Yadda mamacin ya dauki Kiswa da mahimmanci


Mamacin ba kawai rayuwar sa ya bayar ga hidimar Kiswa ga dakin Ka’abar ba, a’a aikinsa yana yinsa cikin karsashi da nishadi da kuma salo. 

ka'aba
Mai rubutun adon Kiswa na Ka’aba Rajab Mahoos  ya rasu bayan hidima ta shekara 47


Ya rasu yana dan shekara casa’in a wani asibitin kudi. Yayi murabus daga aikinsa tun shekarar 2004. Amma duk tsawon rayuwar sa ya tafiyar da ita wajen bada gudummawar yadda ake yin Kiswa din wato adon zinare ga dakin na Ka’aba. 
Haka kuma, ya kasance yana jin wadata da  wannan aikin nasa mai kima. 

Inda mai adon Ka’abar ya rasu


A duk inda ake taron jama’a kuma ya zamto zai fadi wani abu, to zai mike ya fadi cewa shi mai aikin Kiswa ne na Ka’aba, sannan yana kokarin nuna wani karin haske a kan aikin. 


Al Maliki dan sanda  ne kuma mutumin kirki wanda aka san shi kankan da kai da kuma yakana, a kaf cikin tsaransa, kananan sa, da kuma dalibansa. An haife shi ne a wani kauyen kusa da Makka. 


Hakika duniya ta shaida kyawawan adon Kiswa da aka dinga yi wa ka’aba kimanin shekara 50, duk a karkashin kulawar sa.

Tsohon Limamin Ka’aba, Adil Al-Kalbani ya koma harkar fim a gidan talabijin na kasar Saudiyya

A wani gajeren bidiyo mai tsawon minti biyu, tsohon Limamin Ka’aba, Sheikh Adil Al-Kalbani, ya bayyana takaitaccen bayani kan matsayar shi.

Wani fim mai dogon zango mai suna “Combat Field” da aka dauka a birnin Riyadh a cikin wannan shekarar ta 2021, zai nuna tsohon Limamin Masallacin Ka’aba, Sheikh Adil bin Salem bin Saeed Al-Kalbani.

Wannan lamari dai ya jawo maganganu masu yawan gaske a shafukan sada zumunta na zamani, inda aka dinga caccakar tsohon Limamin da maganganu kala-kala.

Sheikh Adil Al-Kalbani ya fito a cikin wani na talla da aka nuno dakarun sojoji a filin daga dauke da makaman yaki. Bidiyon mai tsawon minti 2 da dakika 41 ya nuna tsohon Limamin Ka’abar kuru-kuru a ciki.

Shafin Twitter na hukumar jin dadi da nishadi ta kasar Saudiyya sune suka wallafa wannan bidiyo a shafinsu mai suna Turki Alalshikh. Tsohon Limamin har rubutu ya wallafa a kasan bidiyon, inda yake tambaya cewa:

“Shin kuna ganin zan iya zuwa masana’antar Fina-finai ta Hollywood?”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi