Mayakan ISWAP sun kashe mutane 25 bayan sun farma kauyuka 4 a jihar Borno

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
You are currently viewing Mayakan ISWAP sun kashe mutane 25 bayan sun farma kauyuka 4 a jihar Borno
Mayakan ISWAP sun kashe mutane 25 bayan sun farma kauyuka 4 a jihar Borno

A kalla mayakan gungiyar ISWAP sun kashe mutane 25 a wadansu hare-hare mabanbanta da suka kai a kudancin jihar Barno.

An gano cewa kungiyar ISWAP sun yi wa kauyen Sabon-gari na karamar hukumar Damboa, a ranar Asabar ,inda suka hallaka a kalla mutane 11.

Kauyen yana da kimanin nisan kilomita 125 daga babban birnin Mai duguri.

A fadar jamian tsaro , kimanin gawawwaki bakwai aka fitar a ranar Asabar din kafin daga bisani a kara samun guda hudu.

How to end banditry in Nigeria 1
Mayakan ISWAP sun kashe mutane 25 bayan sun farma kauyuka 4 a jihar Borno

Abu Modu, wani dan rundunar sa kai ta CJTF ya bayyana cewa akwai mace a cikin majikkatan.

“ Mun gano gawawwaki har guda 11 na manoma . Baki daya an harbesu ne a mabanbantan lokuta. A yau za a yi musu suttura kamar yadda addinin musulunci  ya tanadar. Maganar da muke yanzu kauyen sabon gari a yanzu babu kowa. Mutum biyun da aka ji wa rauni yanzu haka suna garin Damboa. Mutane sun kaurace wa kauyen saboda tsoro, “ Ya fada.

Harin ya faru ne sa’o’i 24 bayan an kai wani harin a kauyukan Mandaragirau da Ghuma dake karamar hukumar Biu a jihar Borno.

Kwana biyu kenan kacal bayan harin da aka kai kauyen kautikari ta karamar hukumar Chibok, inda a can kuma aka kashe mutum hudu wanda ya hada har da basaraken gargajiya.

Masu aikin bijilanti na Mandaragirau sun ce wannan ne karo na biyu da yan ta’addan suka farmaki yankin su a cikin watan Fabarairu kadai.

“A kalla mutane 13 aka fillewa kai a kauyen Mandaragirau din dake karamar hukumar Biu a ranar Asabar. Sun zargesu da bayar da bayanai ga sojoji. Muna rokom gwamnati da ta taimaka mana. Ba mu da wani karfi yanzu”,

a fadar wani dan bijilanti.

A fadarsa

”Zuwansu na farko ,an sace wasu samari ne a kauyen namu .Har yau ba’a ji duriyar su ba.

“ A kauyen kuma ,sun sace ‘yan mata biyu da kayan abinci . Sun fasa shaguna ,kuma sun kwashe dabbobi sun tafi dasu”.

Ya bayyana.

Sojojin Najeriya sun fatattaki ‘yan ta’addan ISWAP, sun kwato awaki 500

Dakarun sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai a jihar Borno sun yi nasarar ƙwato awaki 500 a hannun ‘yan ta’addan ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) a ƙaramar hukumar Jere ta jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta samu cewa anyi ‘yar gajeruwar musayar wuta tsakanin sojojin da ‘yan ta’addan na ISWAP, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin mambobin ‘yan ta’addan.

Wata majiya ta bayyana cewa makiyayan sun turo saƙon neman agajin gaggawa ga kwamandan rundunar atisayen Lafiya Dole, Major General Chris Musa, inda su ka sanar da shi satar awakin da aka tafka musu.

Sojojin sun bi bayan ɓarayin awakin inda su ka ritsa su a kusa da wata gonar cashew. Sun yi musayar wuta da su wacce ta yi sanadiyyar mutuwar biyar daga cikin su, yayin da sauran su ka ranta ana kare su ka bar awakin. Majiyar sojin ta tabbatar

Dakarun Najeriya sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP 16 a jihar Borno

A ranar Litinin ne dakarun rundunar sojin Najeriya suka samu nasarar kashe akalla ‘yan ta’addar ISWAP guda 16 a karamar hukumar Jere dake jihar Borno.

Jaridar PR Nigeria ta ruwaito cewa dakarun sun kashe ‘yan ta’addar a kokarin da suke na dakile harin ta’addanci

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi