2023: “Ni matashi ne mai jini a jika”, Tinubu

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
You are currently viewing 2023: “Ni matashi ne mai jini a jika”, Tinubu

Bidiyon Tinubu wanda ya ke shaida wa magoya bayan sa yayin ci gaba da yawon neman amincewa da shi domin zama shugaban ƙasa ya yadu a kafafen sada zumunta, LIB ta ruwaito.

Ɗan takarar shugabancin ƙasa kuma jigon jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa shi matashi ne kuma yana da kuzarin da zai iya shugabancin Najeriya.

2023: "Ni matashi ne mai jini a jika", Tinubu
2023: “Ni matashi ne mai jini a jika”, Tinubu

Tsohon gwamnan Jihar Legas ɗin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da wasu ƴan jam’iyyar APC tare da magoya bayan sa a ƙarshen mako.

Tinubu ya ce APC zata ci gaba da kare muradin ƴan Najeriyan da ke zaune a ciki da wajen ƙasar nan tare da tabbatar da cewa ƙasar ta kasance abisa tafarkin da ya dace.

Ya yi ƙari da cewa yana da halin da zai iya yi wa ƙasar hidima domin ta bunƙasa.

“Na tsaya a gabanku…. kuma Ni matashi ne,” kamar yadda Tinubu yace, yayin da magoya bayansa suke shewa.

Hukuma na neman dan gaban goshin Tinubu, Abdulmumini Jibrin Kofa ruwa a jallo, kan zargin rashin da’a

Hukumar tsara gidaje ta kasa (FHA)  ta gayyaci Abdulmumini Jibril, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, wanda a yanzu yana matsayin darakta mai zartarwa a hukumar, kan zargin rashin rashin da’a.

Takaddar bincike da hukumar ta fitar akan Kofa

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, a wata wasika da shugaban kwamatin bincike da ladabtarwa,  Zubairu Salihu ya fitar, mai kwanan wata 15 ga Fabarairu, yace, Kofan yaki amsa takaddar tuhuma da aka aike masa tun farko.

Daga baya ma, Jibril din ya ci gaba da jagorantar yakin neman zaben tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Ahmad Tunibu, na Shugaban kasa, alhalin yana ma’aikacin gwamnati.

Rikicin Jibril din da hukumar tsara gidaje ta kasa 

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, tun farko, Jibril din shine darakta mai zartarwa dake kula da bangaren hada-hadar kasuwanci kamar(tallace-tallace, kamfanoni, da kuma tsare-tsaren gidaje ), amma yanzu, yana kula da  bangaren bincike, kirkire-kirkire, da kuma ci gaba. 

A cewar rahoton, mahukuntan hukumar, sun nemi sahalewar sa hannun shughukumaaban kasa, domin a rage masa matsayi, banyan sun bata da babban manaja, Gbenga Ashafa.

A karshe dai Abdulmumini Jibrin ya bayyana ainahin inda Tinubu yake samun dukiyar shi

A wata hira da aka yi a gidan talabijin na TVC, an sake jifan Jibrin, tsohon dan majalisar wakilai da tambaya kan cewa menene silar arzikin da Tinubu ya ke da shi.

A martanin da ya mayar, Jibrin ya ce tushen arzikin shugaban jam’iyyar APC na kasa ba wani abun tada zaune tsaye ba ne abu ne da yake a bayyane a fili.

Tun yana karatu ya soma tara arzikin sa

A cewar tsohon dan majalisar, kungiyoyi da dama sun fara farautar Tinubu tun lokacin yana karatun, inda ya bayyana cewa tsohon gwamnan na Legas ya yi aiki da kamfanin Mobil da kuma wasu kamfanoni kafin da ga baya ya tsunduma harkar siyasa.

Jibrin ya kara da cewa Tinubu bai shiga siyasa a tsiyace ba dama da kudin sa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi