Mijin tace: Hotunan wani fitaccen dan siyasa yana shirya wa matar sa abincin kari

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Mijin tace: Hotunan wani fitaccen dan siyasa yana shirya wa matar sa abincin kari
Mijin tace: Hotunan wani fitaccen dan siyasa yana shirya wa matar sa abincin kari

Wani babban dan siyasa a kasar Zambia ya yada hotunan sa yayin da yake hada wa iyalin sa abincin karin kumallo, LIB ta ruwaito.

Dan siyasan kasar Zambia, Chilufya Tayali, ya yada wasu sabbin hotunan sa yayin da yake hada wa matar sa abincin kari.

dan siyasa2
Mijin tace: Hotunan wani fitaccen dan siyasa yana shirya wa matar sa abincin kari

Kamar yadda yace:

“Sai da na nemi rigar mata na sanya domin shigar ta dace da irin aikin da nake yi.”

Yadda aka nada wa Oscar bakin-duka bayan ya yi yunkurin kulla soyayya da matar wani dan siyasa

Wani Andrew Lee Oscar ya ci bakin duka bayan ya yi yunkurin haduwa da matar wani dan siyasa wacce suka hadu a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, Legit.ng ta ruwaito.

Matar ta hanzarta bayyana wa mijin ta abinda mutumin ya ce daga nan ita da mijin suka yanke shawarar yi masa kwanton bauna don ta biye masa ya zurma gadar zare.

Lamarin ya auku ne a Jihar Delta inda matar ta hadu da mutumin wanda ya bukaci su hadu a Facebook.

Wani Victor Kelechi Onyendi ya bayar da labarin a shafinsa na Facebook inda yace mutumin ya bukaci haduwa da matar Honarabul Precious Ajaino wanda darekta ne na kwadago sannan kuma ya rike kujerar shugaban karamar hukumar Ethiope ta yamma.

An samu bayanai akan yadda mutumin ya bukaci fara soyayya da matar auren daga nan ita mijin ta suka yanke shawara ladabtar da shi.

Hukumomin tsaro su fito su bayyanawa jama’a ‘yan siyasar dake daukar nauyin ta’addanci a Najeriya – Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya zargi cewa kokarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi na kawo karshen ta’addanci a Najeriya na samun koma baya ta wajen ‘yan siyasa.

Da yake magana a wajen wani taro da aka gabatar ranar Juma’a 18 ga watan Disamba, Bello yace hukumomin tsaro na kasa ya kamata su fito su bayyanawa duniya mutanen da suke kawo koma baya wajen samar da zaman lafiya a Najeriya.

A cewar mai magana da yawunsa, Mohammed Onogwu, gwamnan yayi kira ga a dauki kwakkwaran mataki akan wadannan mutane.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi