2023: Ina ba mata masu kananun karfi N5000 don ilimin yaran su mata, Tambuwal yayin kamfen

  • Post author:
  • Reading time:4 mins read
You are currently viewing 2023: Ina ba mata masu kananun karfi N5000 don ilimin yaran su mata, Tambuwal yayin kamfen

Gwamna Aminu Takbuwal na jihar Sakkwoto ya bayyana yadda yake biyan mata masu kananun karfi N5,000 ga ko wacce yarinya macen da suka tura makaranta, LIB ta ruwaito.

Aminu Tambuwal 2
2023: Ina ba mata masu kananun karfi N5000 don ilimin yaran su mata, Tambuwal yayin kamfen

Tambuwal ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da TVC na cewa, jihar Sakkwoto tana daya daga cikin jihohin da aka bari a baya bangaren ilimin boko, ya bada labarin yadda ya tilasta ilimi ga kowanne yaro.

Haka zalika, ya ce dokar bada sulallar N5,000 din tana aiki ne, saboda zaiyi wuya iyaye masu kananan karfi su iya samun kwatankwacin wannan kudin.

Tambuwal – Babu wani abu a duniya da zai sa na koma jam’iyyar APC

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya sanar da cewa babu wani abu a duniyar nan da zai saka ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Tambuwal ya bayyana haka a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, a jihar Sokoto, a lokacin da yake caccakar jam’iyyar APC mai mulki akan yadda ta kasa cika alkawuran da ta yiwa ‘yan Najeriya.

Ya kara da cewa ‘yan Najeriya na cigaba da shan wahalar wannan gwamnatin mai mulki ta sanya su a ciki, kamar yadda jaridar Nigerian Tribune.

Gwamnan na jihar Arewacin Najeriya ya bayyana cewa:

Rashin kyakkyawan shugabanci ya jefa ‘yan Najeriya cikin wahala, bakin talauci, da kuma lalacewar ababen more rayuwa.

Tambuwal

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi