Niger: ‘Yan ta’adda sun yi garkuwa da amarya a wajen bikin aurenta, sun kashe wasu 10

You are currently viewing Niger: ‘Yan ta’adda sun yi garkuwa da amarya a wajen bikin aurenta, sun kashe wasu 10
Niger: 'Yan ta'adda sun yi garkuwa da amarya a wajen bikin aurenta, sun kashe wasu 10

A ranar Asabar din da ta gabata ne ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da amarya a wani daurin aure a kauyen Gbacitagi da ke ƙaramar hukumar Lavun a jihar Neja, inda suka kai farmaki a wasu ƙauyukan yankin tare da kashe wasu mutanen ƙauyen 10, wasu daga cikinsu baƙi ne a wurin daurin auren.

Dukkanin kayayyakin da aka kawo domin bikin auren da kuma kuɗi ‘yan ta’addan sun kwashe. ‘Yan bindigar da yawansu ya kai 100, da ke kan babura dauke da nagartattun makamai da suka hada da bindigogi ƙirar AK47 sun afka wa al’ummar .

'Yan bindiga
Niger: ‘Yan ta’adda sun yi garkuwa da amarya a wajen bikin aurenta, sun kashe wasu 10

‘Yan ta’addan sun kuma yi awon gaba da wasu manya-manyan shanu tare da sace kayan abinci a ƙauyukan da suka kai hari.

Wasu ƙauyukan da aka mamaye a cewar rahoton sun hada da Egbako, Ndaruka, Ebbo, Ndagbegi, Tshogi, Gogata da Ndakogitu Tsonfadagabi, Kanko da Gbacitagi.
An gano cewa ‘yan ta’addan sun maƙale a Akere, inda aka ce gadar da ta hada al’umma da Wushishi ta ruguje.

Shanun da suka yi awon gaba da su a cewar rahotanni sun ki tsallakawa zuwa Wushishi ta cikin kogin, lamarin da ya sa ‘yan bindigar suka yi watsi da su tare da bin hanyoyi daban-daban domin tserewa.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto ba a san inda aka yi da amaryar da wasu da aka sace ba.

Kwamishinan kananan hukumomi da tsaro na cikin gida Mista Emmanuel Umar ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin amma ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani ba. An kasa samun ‘yan sanda domin tabbatar da faruwar lamarin.

Jihar na fama da matsalar ‘yan ta’adda

Jihar Neja tana ɗaya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya waɗanda su ke cigaba da fama da matsalar ‘yan bindiga. ‘Yan bindigan sun yi ƙaurin suna wajen kai hare-jare ga mutanen da ba suji ba ba su gani.

Mutane da dama sun rasa rayukan su da dukiyoyin sun tun lokacin da rikicin ‘yan bindiga ya ɓarke a yankunan na Arewacin Najeriya.

‘Yan ta’adda sun halaka mutum 7, sun lalata gada daya tilo da za’a bi a kai musu hari a jihar Kaduna

An halaka kusan mutum bakwai a ranar Talata lokacin da ‘yan ta’adda su ka kai farmaki a wasu ƙauyuka guda uku a ƙaramar hukumar Zangon Kataf cikin jihar Kaduna.

Mai magana da yawun ƙungiyar The Southern Kaduna Peoples Union Public, Mr Luka Binniya, ya tabbatar wa jaridar PUNCH da aukuwar lamarin ranar Laraba.

A cewar sa, ‘yan ta’addan sun ƙona gidaje da dama sannan su ka halaka mutum ɗaya a ƙauyen Zaman Dabo, yayin da aka halaka wasu mutum shida a ƙauyukan Chibob da Sabon Kaura.

‘Yan ta’addan sun buɗe wa mutane wuta

Binniya ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun farmaki ƙauyukan ne cikin gungu mai yawa sannan su ka buɗe wa mazaunan ƙauyukan wuta, inda su ka lalata dukiya mai ɗumbin yawa.

Ƴan ta’addan sun yi amfani da rashin jami’an tsaro a safiyar ranar Talata tsakanin Unguwar Wakili da Abuyab inda su ka lalata gada ɗaya tilo da ta haɗa ƙauyukan biyu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi