Foliteknik din Delta ta hana shiga harabar ta ga mata marasa sanya rigar mama da dan kamfai

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Foliteknik din Delta ta hana shiga harabar ta ga mata marasa sanya rigar mama da dan kamfai
Foliteknik din Delta ta hana shiga harabar ta ga mata marasa sanya rigar mama da dan kamfai

Hukumar makarantar foliteknik ta Jihar Delta da ke Ogwashi-Uku ta hana mata marasa sanya rigar mama ko dan kamfai shiga cikin harabar ta.

Wakilin The Punch ya tattaro bayanai akan yadda jami’an tsaron hukumar makarantar suka hana wasu daga cikin daliban da basu sa rigar mama da dan kamfai ba shiga tun daga bakin kofar makarantar bayan sun bincike su tas.

deltaa poly
Foliteknik din Delta ta hana shiga harabar ta ga mata marasa sanya rigar mama da dan kamfai

Hakan yana da alaka da yadda lamurra marasa dadi suke ta aukuwa a makarantar kamar fyade, kungiyar asiri da kuma yadda masu damfarar yanar gizo suke ta yawaita a makarantar.

Yayin tattaunawa da kakakin hukumar makarantar, Mr. Manfred Oyubigbeye, wakilin The Punch ya tabbatar da yadda kakakin ya ce munanan shigar da dalibai ke yi ne suka janyo wannan tsatstsauran matakin.

A cewarsa:

“Bamu kawo wannan tsarin hakanan kawai ba. Wani lokacin dole hukumar makarantu ko ma’aikatu su yi dubi da yadda mutane suke bayyana a cikin su musamman idan rashin shiga mai kyau ya yawaita.

“Mun ja kunnen dalibai akan shigar su, jami’ar ta dade tana nuna rashin jindadin ta akan shiga mara kyau ga dalibai da kuma malamai. Yanzu haka magatakardar jami’an ya yi magana akan mummunar shigar da dalibai da malamai suke yi. Bama so kuma bama son a dinga yi.

“Yanzu haka makarantar ta dauki wani tsari wanda jami’an tsaron makarantar zasu bincike duk mai shiga makarantar kuma su kori duk wanda suka ga yana shigar banza don ya koma gida ya sauya ta.”

A cewarsa, kwanan nan za a fara hukunta wadanda aka kama da shigar banza don ya zama izina ga wasu.

Sabbin hotunan Maryam Yahaya a Dubai babu rigar mama sun janyo mata zagi

A ranar Juma’a, 18 ga watan Fabrairun 2022 jarumar Kannywood, Maryam Yahaya ta saki sabbin hotunan ta a shafin ta na Instagram ba tare da ta sanya rigar mama ba.

Hotunan sun janyo mata suka da caccaka ko ta ina kafar inda wasu suka dinga zagin ta akan yadda bata dade da murmurewa daga ciwo ba ta fara shigar banza.

Wasu sun dinga yi mata wa’azi suna cewa ya kamata ta yi wa kanta fada ta daina duk wasu ayyuka marasa kyau musamman ganin ko jikin ta bata gama mayarwa ba.

A kwanakin baya jarumar ta yi ciwo wanda mutane da dama suka zaci mutuwa zata yi don duk ta rame ta fita hayyacin.

A lokacin, masoyanta sun dinga yi mata fatan alkhairi da kuma fatan zata natsu, ciwon ya zama izina a gare ta ta gyara rayuwar ta.

Ba wannan bane karon farko da jarumar ta saba yin hotuna ba tare da ta sanya rigar mama ba. Ga masu bibiyarta a Instagram, ta kan saki bidiyoyi ko kotuna sanye da riguna da suke tabbatar da hakan.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi