Ya dace dattawa su shiga tsakanin Air Peace da Masarautar Kano, Kungiyar matasa ta magantu

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
You are currently viewing Ya dace dattawa su shiga tsakanin Air Peace da Masarautar Kano, Kungiyar matasa ta magantu
Ya dace dattawa su shiga tsakanin Air Peace da Masarautar Kano, Kungiyar matasa ta magantu

Shugaban kungiyar Arewa youth ConSultive Forum AYCF, Alhaji Yerima Shettima a cikin wata sanarwa da ya bayyana wa Daily Trust ya ce, “Abin takaici ne a ce har yanzu an kasa sa baki game da rashin fahimtar juna da aka samu da sarkin Kano da kamfanin jirgin sama na Air peace, har yanzu dattawan kasar nan babu wanda ya ce ko kala domin ganin an samu maslaha game da lamarin”.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Yarima Isa Bayero, babban jami’in kula da harkokin mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya zargi kamfanin jirgin Air peace da yi wa Sarkin kano raini, ta hanyar kin jinkirta tashin jirgin saman Air Peace din daga Legas zuwa Kano, bayan da kamfanin ya jinkirta tashinsa daga Banjul, Gambia zuwa garin Legas.

Ya dace dattawa su shiga tsakanin Air Peace da Masarautar Kano, Kungiyar matasa ta magantu
Ya dace dattawa su shiga tsakanin Air Peace da Masarautar Kano, Kungiyar matasa ta magantu

Kamfani Air Peace ya musanta zargin da ake mata

Sai dai kamfanin na Air Peace ya musanta cewa bai mutunta Sarkin ba. Kamfanin ya ce hakan da ya faru ya yi ne don kare martabar kamfanin ta hanyar kin jinkirta jirgin da ke shirin tashi.

Yarima Isa Bayero ya bai wa kamfanin jirgin wa’adin sa’o’i 72 a ranar Asabar din da ta gabata da ya yi azamar neman gafarar Sarkin da kuma al’ummar Masarautar Kano.
Ya ce ya kamata a ce manyan ‘yan Najeriya su gaggauta shiga tsakani ga me da rashin fahimtar juna da ke tsakanin ofishin daraktan kula da kamfanin na Air Peace “domin a samu zaman lafiya dawamammiya”.

Idan ba a manta ba, a ranar Asabar ne aka samu labarin cewa Sarkin Kano ya samu tsaikon jirgin sama da Awa 1 daga Banjul zuwa Legas inda hakan ya hana su shiga jirgin da zai hada su da Kano saboda sun isa Legas saura minti 30 a tashi.

Masarautar Kano ta aike da takarda inda takardar ta yi ikirarin cewa Sarkin Kano ya kira shugaban kamfanin Air Peace, Allen Onyema, domin ya sanar da shi bukatar son a jinkirta tashin jirgin da safe zuwa Kano saboda abunda ya faru a Banjul.

“Kiri-kiri ya ki tare da shan alwashin cewa hakan fa ba zai yiwu ba. Na dauki hakan a matsayin cin mutunci da nuna rashin mutunta mai martaba da kuma al’ummar Kano baki daya,” Sarkin Kano ya rubuta haka a karar da ya kai Mista Onyema.

Sai dai a martanin da ta mayar a ranar Juma’a, Air Peace ta bayyana cewa zargin da ake mata karya ne aka yi ma kamfanin.

Babban jami’in gudanarwa na kamfanin, Toyin Olajide, ya bayar da hujjar cewa, Air Peace na mutunta sarkin Kano, sabanin rade-radin da ake cewa wai an raina sarkin, hakika kamfanin ya kare martabar sarki “ta hanyar kin bin abin da Isah Bayero ya ke so mu yi.”

Sanarwar ta ce: “Da a ce mun amince da jinkirta tashin jirgin da ya shirya tashi, na tsawon awa 1 kawai a bude kofa a jira Sarki ya shiga, hakan na iya janyo cece kuce da maganganu a kafafen yada labarai a fadin kasar inda za su nuna adawa ga kamfanin jirgin sama da kuma shi sarki kan shi. Babu irin rokon da ba mu yi wa Isa Bayero ba amma ya kasa fahimta.

‘Yan sanda sun kwaci wani matashi dakyar a hannun al’umma yayin da suke shirin kashe shi bayan ya yaga Al-Qur’ani a Kano

Wani matashi da yake sana’ar gadi wanda har yanzu ba a bayyana sunan sa ba,yana tsare a hannun ‘yan sanda bisa zargin sa da yaga Alqur’ani mai girma.

Matashin da ake zargin mai kimanin shekaru 20 a duniya, an ce jami’an hukumar Hisbah sune suka kwace shi daga hannun al’ummar unguwar Kuntau da ke cikin birnin Kano.

Daga nan kuma suka mika shi ga ‘yan sanda a halin yanzu dai mutumin yana tsare inda ake gudanar da bincike.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi