Wata sabuwa: Yadda ƙawar amarya tayi wuff da angon ƙawar ta a ranar biki

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Wata sabuwa: Yadda ƙawar amarya tayi wuff da angon ƙawar ta a ranar biki

Wani abu da ya faru wanda ya ɗauki hankulan mutane da dama shine yadda wata ƙawar amarya tayi wuff da mijin ƙawar ta ta a ranar biki.

Yadda lamarin ya auku

Lamarin ya faru ne a unguwar Katsinawa ta Mararraba a jihar Nasarawa. Shaidun ganin da ido sun tabbatarwa da shafin Northern Hibiscus cewa lamarin ya auku ne yayin da amaryar ta ce ta fasa auren inda ƙawarta ba tayi wata-wata ba ta ce ayi da ita.

Nan take aka ɗaura musu aure inda wani mutum ya ba ango kyautar naira miliyan biyu nan take. Mai unguwar wurin ya yiwa ango kyautar kayan ɗaki yayin da abokanan ango su ka biya sadakin naira dubu ɗari da hamsin nan take.

A cikin bidiyon da aka wallafa a shafin an nuno amaryar da ta ce ta fasa auren kwance a gadon asibiti cikin halin damuwa. A yayin da a wata dauƙa daban kuma aka nuno ƙawar ta wacce aka ɗauran auren da ita a wajen biki cikin annashuwa.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su. Ga kaɗan daga ciki:

Kafigwamna ya ce:

Insha Allah tana tashi zata ji har amarya ta yi ciki

@Donutfairy ta rubuta:

To wannan jaje za’ayi ko Allah ya kyauta?

@Real_ismo ya rubuta:

Ta so ta tallata shi amma Allah yace ba yau ba.

@nabeelah____ ta rubuta:

Kayyasa 😂😂😂😂 rabon kwado

@ayeesha_g ta rubuta:

Hmmmm abubuwa na faruwa, ashe daman ta sa ido kenan

Yadda Amarya ta rasa ran ta ana tsaka da daurin auren ta

Wata amarya mai suna Bilkisu Umar Tantoli ta rasu ranar Juma’a 25 ga watan Fabrairun 2022, Muryar ‘Yanci ta ruwaito.

Limamin babban masallacin Juma’a na Nasarawa da ke garin Kaduna, Liman Jabiru Isah Na’ibi ya bukaci dangin amarya da ango su shigo a daura aka sanar da shi cewa Allah ya dauki ran amaryar.

Take anan ango ya shiga mummunan yana yi inda aka zarce da shi gida bayan samun labarin rasuwar amaryar.

Muna fatan Ubangiji ya gafarta mata ya kuma sada ta da mala’ikun rahama, ameen

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi