Wata mata mai juna biyu mai suna Jamila Ardo, ta gurfana a gaban kotu bisa zarginta da yin garkuwa da kanta tare da karɓar kuɗin fansa a hannun masoyinta.
Matar mai suna Jamila Ardo wacce ta fito daga Wauru Jabbe a karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa, ta yi garkuwa da kanta tare da karɓar kuɗi Naira miliyan biyu daga Mallam Adamu Ahmed da ke babban birnin tarayya Abuja.

Matar mai shekaru 25, wacce ake zargi da haɗa baki da wani Abdulaziz wajen yin garkuwa da kanta domin a damfari masoyinta, ta yi nasarar ƙulla makircin nata.
An ce ta yi amfani da kuɗin ne wajen siyan gida
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin da Ahmed sun yi soyayya ne bayan sun haɗu a Facebook, wanda mutumin bai san yana hulda da wata matar aure ba.
PUNCH Metro ta samu labarin cewa duk tsawon soyayyar da suke yi ba su taɓa haɗuwa da juna ba, amma alaƙar ta bunƙasa yayin da suke ci gaba da tuntubar juna ta yanar gizo.
Cikakkun almundahanar, kamar yadda yake ƙunshe a cikin takardar tuhumar, ya nuna yadda Abdulaziz, a lokacin da yake ganawa da Ardo, ya kirawo masoyinta a waya, inda ya shaida masa cewa an yi garkuwa da ita, kuma ya buƙaci a biya ta kuɗin fansa.
Yayin tattaunawar neman a sake ta, an ce Adamu ya ji Ardo na kuka yayin da ta roƙe shi a waya ya biya kuɗin fansa.
An ce Adamu ya ajiye kuɗin ne a asusun banki mai suna Amina Mohammed.
“Bayan ya aika da kudin ne sai masoyiyar sa ta sanar da Adamu cewa masu garkuwa da mutane sun sako ta.”
“Duk da haka, Adamu ya yi shakku kuma ya shigar da ƙara a ofishin binciken jihar a ranar 16 ga Nuwamba, 2021,” in ji tuhumar.
Daga baya ‘yan sanda sun kama mai asusun bankin da aka yi amfani da su wajen karɓar kuɗin fansa, Mohammed.
Kafin fallasuwar wannan labari, an ruwaito mijin Ardo ya tambaye ta hanyar samun kudin shiga, saboda ta yi iƙirarin cewa ‘yan uwanta sun aiko da kudin.
Daga nan aka kama ta kuma aka gurfanar da ita a gaban babban kotun majistare na Yola bisa laifin haɗa baki da garkuwa da mutane, saɓanin sashi na 60 da 248 na dokar Penal Code.
Ta musanta aikata laifin
Dan sanda mai shigar da ƙara, Sufeto Abubakar Nurudeen, ya roƙi Alƙalin kotun, Abdullahi Digil, da ya ɗage sauraron ƙarar don baiwa masu gabatar da ƙara damar miƙa ƙarar zuwa ofishin kula da ƙararrakin jama’a domin samun shawarar lauya.
Lauyan wanda ake ƙara, C. Crowealth, wanda ya bayyana tare da T. K. David, ya roƙi kotun da ta baiwa wacce ake karewa damar zuwa wurin kiwon lafiya duba da yanayin da take ciki.
Crowealth ya kuma buƙaci kotun da ta umurci masu gabatar da kara da su ba su duk wasu takardun da suka dace don ba su damar yin shiri don kare kansu.
Alƙalin kotun, Digil ya amince da bukatar kuma ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 10 ga Maris, 2022, yayin da ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake ƙara.
Angon mata takwas yana rayuwa cikin farin ciki da annashuwa
Wani ango mai sana’ar zanen Tattoo ɗan ƙasar Thailand ya bayyana cewa yana zaune a gidansa tare da matansa guda takwas duk ’yan mata waɗanda ya aure su kusan lokaci ɗaya labrin da ya dauki hankalin jama’a sosai a Intanet.
Angon mai suna, Ong Dam Sorot, matashi ne mai zanen Tattoo da ya ƙware a zanen gargajiya na ‘yantra’ na asalin addinan Indiya, kwanan nan ya gana da wani sanannen dan wasan ban dariya na ƙasar Thailand don yi hira game da matakin aurensa mai cike da kace- nace.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com