27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Da duminsa: Jaruma Hafsat Idris Barauniya ta yi auren sirri

LabaraiKannywoodDa duminsa: Jaruma Hafsat Idris Barauniya ta yi auren sirri

Fitacciyar tsaleliyar jarumar Kannywood, Hafsat Idris wacce aka fi sani da Barauniya ta yi auren sirri.

LabarunHausa.com ta samu nasarar tattaro bayanai akan yadda jarumar ta yi aure ba tare da ta yada ba ko a shafin ta.

barauniyaa
Da duminsa: Jaruma Hafsat Idris Barauniya ta yi auren sirri

Jarumar bata wallafa hotunan katin auren ta ba, sannan bata fitar da sanarwa ko wani bayani akan wanda zata aura ba.

Sai dai a ranar Asabar da dare, abokan sana’arta kamar Rukayya Dawayya, Samira Ahmed da sauran su suka dinga yi mata fatan alkhairi.

Har ila yau, Shafin Kannywood celebrities na Instagram ya wallafa hoton ta tare da yi mata fatan alkhairi.

Muna fatan Allah ya kade fitina kuma yasa su zauna lafiya, Ameen.

Bidiyon yadda aka gudanar da shagalin sunan jikar Jaruma Hafsat Idris (Barauniya) ranar Laraba

Jarumar fina-finan Kannywood, Hafsat Idris wacce aka fi sani da Barauniya ta yi gagarumar liyafa a ranar Laraba bayan diyar ta wacce ta aurar a shekarar da ta gabata ta haihu.

Shagalin sunan wanda ya samu halartar manyan jarumai tsofaffi da sabbi yadauki hankali kwarai. Cikin jaruman da suka yi wa Hafsat kara akwai Rukayya Dawayya, Samira Ahmad, Mansura Isah da sauran su.

Kamar yadda jarumaHafsat Idris ta wallafa bidiyoyi wadanda ta dauki wankan ban mamaki a shafin ta na Instagram, an ga sauran jarumai suna tikar rawa.

ta wallafa yadda aka sanya wa jaririyar suna ‘Hafsat’ wato takwarar ta wanda hakan ya yi matukar sanya ta farin ciki.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe