Wata amarya mai suna Bilkisu Umar Tantoli ta rasu ranar Juma’a 25 ga watan Fabrairun 2022, Muryar ‘Yanci ta ruwaito.
Limamin babban masallacin Juma’a na Nasarawa da ke garin Kaduna, Liman Jabiru Isah Na’ibi ya bukaci dangin amarya da ango su shigo a daura aka sanar da shi cewa Allah ya dauki ran amaryar.

Take anan ango ya shiga mummunan yana yi inda aka zarce da shi gida bayan samun labarin rasuwar amaryar.
Muna fatan Ubangiji ya gafarta mata ya kuma sada ta da mala’ikun rahama, ameen.
Daga Sani Yusuf Nasarawa, kamar yadda shafin Muryar ‘Yanci na Facebook ya ruwaito.
Miyagun ‘yan bindiga sun yi garkuwa da amarya da wasu mutum 5 a Kaduna
Wasu miyagun ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Rigachikun da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da wata amarya da aka kusa auren ta da wasu mutane biyar.
An rawaito cewa ‘yan bindigar sun afkawa al’ummar da ke kusa da madatsar ruwan kasan da misalin ƙarfe ɗaya na safiyar ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu, inda suka far wa gidaje uku tare da tasa ƙeyar waɗanda abin ya shafa zuwa inda ba a sani ba.
Wata mata da jikokinta na cikin waɗanda aka sace tare da amaryar da aka bayyana sunanta da Khadija. Tana kwance a gefenta lokacin da ‘yan bindigan suka shiga ɗakin su.
“Muna cikin bacci suka shigo daki suka ce Khadija da Shabilu su taho tare da su, kuma suka kwashe waya da biredi a teburin, duk muka rude.” Ta shaida wa Aminiya.
Wani shugaban al’ummar yankin, Idris Abdulrasheed, ya ce lamarin shi ne na farko a cikin al’ummar kuma tuni suka sanar da ‘yan sanda lamarin.
Ya ce har yanzu ‘yan fashin ba su tuntubi iyalan wadanda abin ya shafa ba.
A halin da ake ciki, wani Comr Jameel Abdulkarim, ya bayyana ɗaya daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da shi a matsayin Muktar Abdulsalam.
Muktar a cewarsa, shi ne mataimakin Shugaban Hukumar SUBEB a Kaduna.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com