Yadda ‘yan bindiga sun bude wa masu zaman makoki wuta

  • Post author:
  • Reading time:7 mins read
You are currently viewing Yadda ‘yan bindiga sun bude wa masu zaman makoki wuta
Boko Haram ta ƙaddamarwa kwamandojin ISWAP 10 a yankin tafkin Chadi

‘Yan sandan jihar Anambra sun tabbatar da farmakin da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne suka kai yankin Ebenebe a arewacin karamar hukumar Auka dake jihar Anambra, PMNewsnigeria ta ruwaito.

Wata majiya ta labarta wa Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) yadda lamarin ya auku, yayin da ake tsaka da makokin wani mutum mai shekaru 34, wanda shi ma ake zargin ‘yan kungiyar asirin suka hallaka shi a ranar 30 ga watan Disamban 2021.

yan bindiga
Yadda ‘yan bindiga sun bude wa masu zaman makoki wuta

Marigayin ya rasa ran sa ne a yankin Amansea da ke arewancin Awka.

“Ana tsaka da makoki a gidan marigayin, wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne suka hallara wurin, inda suka bude wa ‘yan zaman makoki wuta,” a cewar majiyar.

Haka zalika, ya bayyana yadda mutane suka samu raunukan alburusan da ‘yan bindiga suka harba, wanda daga bisani aka garzaya dasu asibitin koyarwa na Chukwueneka Odunegwu Ojukwu a Amaku da ke Auka.

“Dan uwa na yana daya daga cikin wadanda aka raunana, muna asibiti tun 11:00 na safe, don ganin mun tabbatar ya dawo hayyacin sa,” a cewarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya bayyana wa manema labarai yadda mummunan al’amarin ya auku, yayin da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne suka bude wa mutanen dake yankin wuta.

“A halin yanzu, bani da masaniya game da wadanda ibtila’in ya auka musu, amma zan sanar muku da zarar na samu cikakken bayani,” a cewarsa.

Ikenga ya kara da bayyana yadda kwamishinan ‘yan sandan Anambra, Mr Echeng Echeng ya shirya tawagar jami’an tsaron daga bangarori daban-daban don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Sheikh Gumi: Kuskure ne bude wa ‘yan bindiga wuta da gwamnati ke yi, saboda su ma a shirye suke

Fitaccen Malamin addinin Musulunci Sheikh Gumi ya soki gwamnati kan harin da take kai wa ‘yan bindiga a daji, inda ya baayyana cewa babu abinda hakan zai jawo illa sake tabarbarewar tsaro a kasa, saboda a cewar shi su ma a shirye suke.

Shahararren Malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi, ya yiwa jami’an tsaro da gwamnati baki daya gargadi akan su dakata da harin da suke kai wa ‘yan bindiga a dazuka, saboda a cewar shi hakan zai kawo wata gagarumar matsala a kasa.

A rahoton da jaridar Premium Times ta ruwaito, Sheikh Gumi ya sanar da cewa da idon shi ya ga irin shirin da ‘yan bindigar suke da shi a lokacin da ya bi su daji yake yi musu wa’azi, saboda haka kokarin da gwamnati ke yi na ganin bayan su zai kawo fitina ne a kasa.

An yi kokarin kawo karshen su a baya, hakan bai yiwu ba sai ma kara samun matsalar tsaro da aka yi a lokacin. Yanzu idan aka cigaba da haka za su fada harkar ta’addanci kai tsaye, shikenan kuma sai a koma gidan jiya.

‘Yan bindiga sun fara daukar matasa aiki a jihar Katsina – Gwamna Masari

Sheikh Gumi ya jima yana kira da ayi sulhu da ‘yan bindiga

Shehun Malamin dai ya jima yana kira ga gwamnati da maimakon a yaki ‘yan bindigar kamata ya yi a bisa da lallama, sai dai gwamnatocin jihohin Zamfara da Katsina sun yi kokarin ganin sun bi wannan shawara ta shi, amma hakan bai canja komai ba, sai ma kara samun tabarbarewar tsaro da aka cigaba da samu a yankunan.

Garkuwa da daliban makaranta ya ta’azzara, kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba ya karu, sakamakon wannan shawara ta shi ya sanya komai ya sake dagulewa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi