Angon mata takwas yana rayuwa cikin farin ciki da annashuwa

You are currently viewing Angon mata takwas yana rayuwa cikin farin ciki da annashuwa
Angon mata takwas yana rayuwa cikin farin ciki da annashuwa

Wani ango mai sana’ar zanen Tattoo ɗan ƙasar Thailand ya bayyana cewa yana zaune a gidansa tare da matansa guda takwas duk ’yan mata waɗanda ya aure su kusan lokaci ɗaya labrin da ya dauki hankalin jama’a sosai a Intanet.

Angon mai suna, Ong Dam Sorot, matashi ne mai zanen Tattoo da ya ƙware a zanen gargajiya na ‘yantra’ na asalin addinan Indiya, kwanan nan ya gana da wani sanannen dan wasan ban dariya na ƙasar Thailand don yi hira game da matakin aurensa mai cike da kace- nace.

Mata takwas
Angon mata takwas yana rayuwa cikin farin ciki da annashuwa

Ango Sorot, ya auri mata takwas kuma suna zaune a gida ɗaya kuma suna ɗaukar kansu a matsayin iyali guda cikin farin ciki da kwanciyar hankali.

Hirar wadda aka sa a shafin Youtube, kawo yanzu ta samu ra’ayin jama’a sama da miliyan 3 a shafin.

Ong Dam Sorot, ya gabatar da matan nasa ɗaya bayan ɗaya tare da bayyana yadda suka hadu. Matan takwas dai sun nuna mijin nasu a matsayin mai matuƙar kirki, mai kula da al’umma, kuma sun yi ikirarin more rayuwa.

Ta yaya Ango Sorota ya hadu da matansa takwas?

Angon ya haɗu da matarsa ta farko, Nong Sprite a lokacin bikin wani abokinsa kuma ya nemi aurenta da gaggawa.

Ta biyu mai suna Nong L, sun haɗu a kasuwa, sai Nong Nan, matarsa ta uku sun haɗu a asibiti.

Daga ta huɗu zuwa ta shida sun haɗu ne a shafukan sada zumunta na Instagram da Facebook da TikTok. Sai matarsa ta bakwai, Nong Film, sun haɗu ne bayan ya gan ta a lokacin da ya ziyarci wajen bauta na Phra Pathom Chedi tare da mahaifiyarsa, yayin da matarsa ta takwas kuma ta karshe, Nong Mai ya hadu da ita lokacin hutu a birnin Pattaya tare da matansa huɗu.

“Watakila shi ne mutumin da ya fi kowa kulawa da muka taɓa gani,” matan takwas duka sun aminta da shi.

Angon ya kara da cewa yana mu’amala da su sosai har ba su da wani abu da za su yi musu ko gardama a kai.

Biyu daga cikin matan Ango Sorot suna da juna biyu a yanzu, kuma yana ɗa da tare da matarsa ta farko, Nong Sprite.

Matan suna kwana a dakuna huɗu, biyu a kowane daki, kuma suna jiran lokacinsu don raba kwanciyar aure da mijinsu.

A bayyane yake, babu wanda ke da matsala da tsarin mijin. Da yake magana a karon farko Ong Dam Sorot ya ce lokacin da ya kawo yiwuwar auren mace ta biyu, Nong Sprite ta ce, tana sonsa matuka kuma ta aminta da aurensa, musamman da yake a kowane lokaci yana mai da hankali kan tambayar ta ko ta yadda da ra’ayinsa.

Ta ce, ta yarda matsawar idan ya kawo matarsa ta biyu, ita ce za ta fara karɓar ta. Sauran bakwai ɗin da suka amince za su aure shi suna da masaniyar yana da aure, yawancinsu kawai sun ce, suna matukar sonshi kuma sun yarda da shi.

Angon Ƙyaƙƙyawan mutum ne, mai hankali kuma ya tabbatar da cewa zai iya kula da su.

Duk da cewa, waɗansu daga cikin matan sun samu matsala wajen faɗawa wa dangin su cewa, suna auren miji mai mace fiye da ɗaya, ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen auren Ong Dam Sorot, kuma a ƙarshe abokansu da danginsu sun amince da lamarin.

A lokacin zantawa da Ong Dam Sorot ya ce, ya shaida wa matan sa cewa su kasance masu gaskiya koyaushe. Idan sun samu wani abu da ba su gane ba su zo su faɗa masa.

Yana tambayarsu sau uku idan sun tabbatar suna son rabuwa da kowa sai shi, idan suka amsa ‘eh’, sai su kasance tare. Har yanzu wani abu na rabuwa bai faru ba.

Mr. Sorot, wanda yake da shahararren shafinsa na sada zumunta da kuma tashar YouTube, ya ce a kullum mutane suna tunanin cewa, shi mai kuɗi ne? kuma zai iya kula da iyalansa, amma ya ce ba gaskiya ba ne.

Kowane a gidansu yana da aikin da ya rataya a wuyansa, kuma matansa suna samun abin da ake ajiyewa ta hanyar yin ayyuka, ko sayar kayayyaki daban-daban, tun daga abinci zuwa kayan kwalliya da kayan aikin hannu.

Sai da tsarin rayuwar aure na Ong Dam Sorot ya haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta, inda waɗansu suka nuna jin dadinsu ga mai zanen da ya haɗa zaman gidansa da matansa takwas, yayin da waɗansu kuma suka nuna masa cikin zolaya cewa “ba mace ɗaya ba, mata takwas!”

Dan Najeriya da ya bata, ya dawo gida bayan shekara 5, ya tarar matarsa ta amarce da sabon ango

An jefa wani dangi a Najeriya a cikin rudani sakamakon dawowar wani dan su da a shekarun baya aka bayyana batansa da kuma mutuwarsa.

Dan Najeriyan wanda ya bata a yayin tafiya a kwale-kwale a kasar Kamaru, ya dawo gida bayan shekara biya inda ya samu har matarsa ta sake yin aure. 
Kokarin da yake yi na sake dawo da matarsa ya ci tura saboda ita bata son rabuwa da sabon mijin nata.

Bayan share shekaru biyar 5 a kasar waje, wani dan NaJeriya ya dawo gida, inda ya tarar matarsa ta kufce masa saboda ta sake sabon aure. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]m

Rubuta Sharhi