Bayan mutuwar aurenta sau 3, Bazawara ta maka mahaifinta kotu kan zai kara yi mata auren dole

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Bayan mutuwar aurenta sau 3, Bazawara ta maka mahaifinta kotu kan zai kara yi mata auren dole
Bayan mutuwar aurenta sau 3, Bazawara ta maka mahaifinta kotu kan zai kara yi mata auren dole

A ranar Laraba, wata matashiya mai shakaru 25, Sadiya ta maka mahaifinta Malam Usman kotun musuluncin da ke Rigasa a Jihar Kaduna, bisa zargin sa da yi mata auren dole, LIB ta ruwaito.

Mai karar, wacce take zaune a yankin Rigasa dake Kaduna, ta bayyana wa kotun cewa wannan ne auren ta na uku.

bazawara
Bayan mutuwar aurenta sau 3, Bazawara ta maka mahaifinta kotu kan zai kara yi mata auren dole

A cewarta:

“Mahaifi na ya shirya yi min auren dole ba tare da nasan mutumin da zan aura ba.

“Aurena na farko, na biyu da na ukun, duk akan dole mahaifina ya min.

“Bazan iya ci gaba da rayuwa haka ba don haka nake rokon kotu da ta raba auren nan.”

Ta bayyana wa kotu yadda take zaune da wani a Unguwan Sarki da ke jihar.

A bangaren mahaifin nata, ya ce diyar shi dakanta ta gabatar musu da mutumin, amma daga bisani tace batason shi.

A cewarsa, batun bata taba ganinsa ba, ba gaskiya bane.

Ya kara da cewa:

“A halin yanzu, ban san inda diyata ke zama ba. Ta bar gidana a ranar auren. Ina rokon kotu da ta umarceta da ta gaggauta dawowa gida.”

Alkali mai shari’a, Malam Salisu Abubakar-Tureta bai amince da bukatar wanda ake karar ba, sai dai ya umarci wacce take karar data koma karkashin kulawar mai anguwan Rigasa.

Daga bisani ya dage sauraron karar zuwa 10 ga watan Maris don ba mai karar damar gabatar da shaidu.

Labari mai dadi: An rage farashin aure a Dawakin Tofa, jihar Kano

A yayin da samari da dama suke korafi akan yanayi na wahalar aure, musamman wajen hada kayan aure dalilin tsadar rayuwa da ake ciki a wannan zamani.

A Arewacin Najeriya dai ana fama da matsalar yawaitar marasa aure da kuma yawan sake-saken aure da ake ta fuskanta tsakanin ma’aurata, wannan dalili ne ya sanya wata karamar hukuma a jihar Kano ta dauki matakin magance wannan matsaloli, musamman ma tsadar aure.

An hana hira da budurwa ba tare da ganawa da iyayenta ba

A wani rahoto da muka ci karo dashi a shafin yanar gizo na Dala FM Kano sun ruwaito cewa shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai ya rage farashin aure a fadin karamar hukumar.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa daga yanzu babu wani saurayi da zai sake kula budurwa, ba tare da yaje ya gana da iyayenta ba.

An sauke farashin aure a Dawakin Tofa

Dangane da batun kayan lefe kuwa, shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa an kayyade kayan zuwa akwati uku kacal.

Majalisar karamar hukumar ta Dawakin Tofa, ta sanya hannu a wannan sabuwar dokar, sakamakon shawarwari da tayi da masarautar Bichi, wanda a karshe majalisar ta kafa kwamiti ta musamman wacce za ta tabbatar da dokar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi