An ga wani Lakcara a jami’ar Abuja yana rawa da nishadi a wani salo na ban dariya, a wani faifan bidiyo da ya karade yanar gizo.
Faifan bidiyon ya nuna malamin jami’ar yana rawa ta ban dariya, a yayin bikin jami’ar na yaye dalibai
Bidiyon ya baiwa mutane da yawa dariya, kasantuwar yadda yake yin rawar kana gani kasan ba kwararre bane kuma ya sha banban da yadda ake yin rawa.

Wani Lakcara a, jami’ar Abuja UNIABUJA, ya tiki rawa akan dandalin gabatarwa wanda sakamakon haka yasa yan kallo suka bushe da makyakyaciyar dariya.
Lakcaran ya yi rawar ne cikin annashuwa yayin bikin yaye dalibai na jami’ar, inda ya jadda hankalin daukacin mahalarta taron.
Yadda rawan ya kasance
Lakcaran wanda yayi shigar dogayen kaya, yana yin rawar ne shi kadai, sannan sai ya dan tsaya ya dan yi magana da mutumin dake tsaye kusa da shi, kamar yana gayyatar sa suyi rawar tare.
Sharhin yan soshiyal midiya akan rawar Lakcaran
Dora faifan bidiyon ke da wiya, wanda @gossipmillnaija suka yi a instagram, sai aka fara samun sharhin ban dariya daga jama’a. Ga kadan daga cikin su :
@zayee_nab yace :” Yayin da yan wahalar daliban ka suka kammala”
@iamperryblink yace: ” Mutum shi kadai kawai ya kama rawa ba tare da kida ba, hakan ya bayyana mini abubuwa da yawa”
@rolat_abiola_olaide yace :
” wadanda suka fi kowa kin ji zasu fita”.
@_Monica yace:
” Ba’a ce haka ba. Ku ka sani ba ko da akwai dan sa a cikin daliban “.
@charming._caramel yace:
“Lakcarori suma mutane ne, suna da bukatar jin dadi da nishadi”.
Obasanjo yayi rawa da jarumar fim ta yan kudu Doyin Kukoyi
A wani labari makamancin wannan da Legit.ng suka ruwaito, anga tsohon shugaban kasar tarayyar Nageriya Olusegun Obasanjo, yana rawa da wata jarumar finafinan kudancin Nageriya (Nollywood ) Doyin Kukoyi.
Tsohon shugaban kasar, ya tiki rawar kuma yayi ta dakyau sosai, harma mutane na cewa yafi jarumar iyawa.
Tsohon shugaban mai shekara 85, yayi wani juyi ta baya, wanda yasa mutane suka yi ta magana a kafar yanar gizo.
Yadda Lakcara ya dinga amfani da almakashi yana yiwa daliban da suka yi askin gayu aski a tsakiyar aji
Wani Lakcara yayiwa dalibi dake jami’ar Veritas a Abuja aski kyauta bayan ya shiga aji da askin kai yaci kudi.
Anga Lakcaran yana amfani da almakashi, inda yake yanke cibiri-cibirin kan dalilin. Amma ba’a saniba ko dokar jami’ar ce bata yarda da hakanba?
Yan Nageriya ciki harda jaruma Nancy Iheme da kuma OAP Daddy Freeze, sun nuna bacin ransu akan lamarin, ta fuakoki da dama.
A wani bidiyo da ya karade yanar gizo, anga wani Lakcara yana aske kan dalibi a cikin ajinsu dake jami’ar Veritas a Abuja.
Abin da ba’a saniba shine ko hukumar jami’ar ce ta haramta tara suma mai cibiri-cibiri. Jama’a da yawa sunyi tir da abin da Lakcaran yayi, inda suke cewa ya kamata a bar maza su yi irin askin da suke so da sumarsu.
A cikin bidiyon da @instablog9ja suka yada a Instagram, anga Lakcaran yana amfani da almakashi yana datse cibiri-cibirin da dalilin ya tsayar akan sa tsebebe.
Mutane da yawa sunyi tir da Lakcaran
Mutane da yawa sun nuna fushinsu akan lamarin, ta hanyoyi da dama.
Haka kuma a wani jaridar Legit.ng sun ruwaito cewa, wani Lakcara a jami’ar Legas, Akoka, ya sasanta rigimar wasu ma’aurata a cikin aji.
A wani bidiyo da shima yayi tashe, anga wani magidanci ya durkusa akan gwiwoyin sa yana rokon wata yarinya gafara, matar da ake rokon taki cewa uffan.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com