24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Abubakar Bashir Mai Shadda zai yi wuff da Jaruma Aishatul Humaira

LabaraiKannywoodAbubakar Bashir Mai Shadda zai yi wuff da Jaruma Aishatul Humaira

Yanzu-yanzu jaruma Aishatul Humaira ta wallafa zuka-zukan hotunan da suka dauka da furodusa Abubakar Bashir Mai-shadda a shafin ta na Instagram.

Dama cikin kwanakin nan labarin Mai-Shadda zai yi aure ya dinga bazuwa a shafukan sada zumunta daban-daban.

mai shadda
Abubakar Bashir Mai Shadda zai yi wuff da Jaruma Aishatul Humaira

Akwai wadanda suka dinga cewa shi ne zai auri Jaruma Aisha Tsamiya, sai dai da safiyar Lahadi suka daga Aishatul Humaira har Abubakar Mai-shadda suka wallafa Pre-wedding pictures din su.

Jarumai da dama da sauran mutane sun dinga yi musu fatan alkhairi.

Auren nasu ya ba kowa mamaki duk da dai masu bibiyar shafinta zai kula tana yawan wallafa bidiyoyin ta tare sa shi suna bin wakoki.

Amma babu wanda ya kawo cewa aure zasu yi kuma lamarin ya zo gab.

A karkashin wallafar da Aishatul Humaira ta yi a Instagram, ta rubuta “save the date”.

Allah ya nuna mana lokacin kuma ya bada zaman lafiya, Ameen.

Nazir ka keta mutuncin mu, kuma ka keta mutuncin masana’antar mu ta Kannywood – Abubakar Bashir Mai Shadda

A yayin da Daraktoci da Furodusoshi suka yi caa akan jaruma Ladi Cima suna yi mata raddi a maganar ta, wacce ta bayyanawa BBC Hausa cewa ba a taba bata kudin da ya wuce dubu biyar ba a duk shekarun da ta kwashe tana fitowa a cikin fina-finan Kannywood.

Fitaccen Mawakin nan Nazir M Ahmad ya fito ya goyi bayan ta, inda maganar shi tafi karfi kan jarumi Ali Nuhu da Falalu A Dorayi, da suka fito suka ce suna bawa jarumar kudade masu kauri a duk lokacin da suka sanya ta a fim.

Maganar Nazir ba ta yiwa ‘yan Kannywood dadi ba

To sai dai kuma maganar ta Nazir ba a nan ta tsaya ba, domin kuwa ya bayyana cewa shi da kanshi shaida ne akan abubuwan dake faruwa a masana’anatar, inda har ya bayyana cewa wannan dalili na zulunci shine yasa ake samun koma baya a masana’antar.

Haka kuma Nazir Sarkin waka ya bayyana cewa wasu ma sune suke cire kudi a aljihunsu su biya domin a saka su a fim, ko kuma idan mace ce, sai ta bada jikinta an kwanta da ita kafin a saka ta a cikin fim.

To sai dai kuma wannan magana ta Nazir ba ta yiwa da yawa daga cikin jarumai da daraktocin na Kannywood ba, domin kuwa bai jima da sakin wannan bidiyo na shi ba, fitaccen daraktan nan Abubakar Bashir Mai Shadda ya fito yayi masa martani a wani bidiyo.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe