27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Ayyiriri: Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya zata yi aure a ranar Juma’a mai zuwa

LabaraiKannywoodAyyiriri: Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya zata yi aure a ranar Juma’a mai zuwa

Fitacciyar tsaleliyar jarumar Kannywood, Aisha Aliyu wacce aka fi sani da Aisha Tsamiya zata yi aure.

Alamu na nuna cewa wani babban mutum zata aura kamar yadda jita-jitar yake ta yawo, Kannywoodcelebrities suka wallafa.

ayshaa tsamiya
Ayyiriri: Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya zata yi aure a ranar Juma’a mai zuwa

Tuni Jaruman Kannywood kamar Zainab Indomie, Ali Nuhu da sauran fitattun jarumai suka fara yi matafatan alheri.

Sannan shafin Kannywoodcelebrities sun wallafa hoton jarumar a Instagram da Facebook suna yi mata fatan alheri.

Kowa ya san yadda jarumar take da natsuwa don mutane da dama suna shaidar ta da kasancewa mai kamun-kai da girmama jama’a.

Muna mata fatan Allah ya ba su zaman lafiya da kwanciyar hankali kuma yasa tsawon rai aka yi mawa.

Cikin dan datsin nan, jaruman Kannywood da dama suna ta yin aure, cikin su akwai jaruma Maryam Wazira, wacce aka fi sani da Laila a shirin fim din Kwana Casa’in, Shu’aibu Lawan kumurci wanda bai sake aure ba tun rasuwar matarsa tsawon shekaru.

Da fatan Allah ya ba su zaman lafiya, Ameen.

Wasu na alakanta tallar maganin mata ‘kaca-kaca’ da Jaruma Umma Shehu ta yi da zargin lalatar matan Kannywood

Tun a makon da ya gabata rigima ke ta ruruwa a masana’antar Kannywood bayan mawaki kuma jarumi, Naziru Sarkin Waka ya zargi jarumai mata da bayar da kudi ko kuma jikin su don a haska su a fim.

Zargin ya yi matukar hassala su inda wasu suka fito suka yi masa wankin babban bargo suna cewa ya janye kalaman sa ko su maka shi a kotu.

Duk da dai jarumar bata da aure, amma an gan ta tana tallata magungunan mata na wata “Jarumar Mata” wacce ta yi fice a kafar Instagram.

Wani ma’aboci amfani da kafar Facebook kuma sananne, Datti Assalafy ya yi shimfida sannan ya wallafa bidiyon Umma Shehu tana tallata magunguna irin wadanda a cewarta mace ko ta gama lalata da maza zata koma tamkar budurwa.

Kamar yadda ya yi wallafar wacce ya yi wa take da: “MAGANAR NAZIRU AKAN WASU MATAN HAUSA FIM GASKIYA NE”.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe